Mutum 100 sun mutu a hatsarin jirgin ruwa a Kwara

Daga BASHIR ISAH

Aƙalla mutum 100 aka ruwaito sun mutu a wani hatsarin jirgin ruwa da ya auku ranar Litinin a Jihar Kwara.

Bayanai sun ce hatsarin ya auku a yankin ƙauyen Egbu da ke cikin Ƙaramar Hukumar Patigi a jihar.

An ce hatsarin ya auku ne a lokacin da waɗanda iftila’in ya rutsa da su a lokacin da suke hanyar komowa gida daga bikin aure da suka halarta a Jihar Neja mai maƙwabtaka da jiharsu.

Tuni Gwmnan jihar, Abdulrahman Abdulrazaq, ya bayyana alhini da ta’aziyya ga ‘yan uwan waɗanda suka rasu a hatsarin.

Sanarwar da Sakataren Yaɗa Labarai ga Gwamnan, Rafiu Ajakaye, ya fitar a ranar Talata, ta nuna galibin waɗanda lamarin ya rutsa da su mazauna ƙauyukan Ebu, Dzakan, Kpada, Kuchalu da kuma Sampi ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *