Sbugaban Majalisar Dattawa ya ziyarci Tinubu bayan rantsar da shi

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ziyarci Shugaban Ƙasa Bola Tinubu a fadarsa da ke Abuja.

A ranar Talata sanatoci suka zaɓi Akpabio na Jam’iyyar APC daga Jihar Akwa Ibom tare kuma da rantsar da shi a matsayin Shugaban Majalisar Dattawa zubi na 10.

Akpabio ya lashe zaɓen ne da ƙuri’u 66 inda ya doke babban abokin hamayyarsa, Abdullazeez Yari na Jam’iyyar APC daga Zamfara, wabda ya samu ƙuri’u 43.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *