Mutum 12 sun mutu, 28 sun jikkata sakamakon hatsarin mota a Zaria – Hukuma

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa ta ce aƙalla mutum 12 sun mutu sannan 28 sun tagayyara sakamakon hatsarin mota da ya ritsa da su a babbar hanyar Zaria zuwa Kano.

Shugaban hukumar na Jihar Kaduna, Kabir Nadabo ne ya bayyana haka a ranar Litinin.

Nadabo ya ce hatsarin ya auku ne a yankin ƙauyen Tashar Yari da misalin ƙarfe 7:36 na safe

Ya ce tirelar da lamarin ya shafa mai lambar rijista KTG 454 ZZ na kan hanyarta ta zuwa Kano ne inda ta gamu da hatsari.

Ya bayyana cewa, yin obatekin ba bisa ƙa’ida ba da gudun wuce misali da kuma ɗaukar kaya wuce kima su ne dalillan da suka haifar da hatsarin wanda ya yi ajalin mutane da dama.

Kazalika, jami’in ya ce Shugaban Ƙaramar Hukumar Makarfi da shugaban hukumar a Tashar Yari, sun halarci wurin da hatsarin ya faru.

Haka nan, ya ce bincikensu ya gano mutum 40 ne hatsarin ya ritsa da su, 12 sun mutu yayyin da 28 sun jikkata.

“An kwashi waɗanda suka jikkata zuwa Babban Asibitin Makarfi don yi musu magani,” in ji jami’in.