Ina da saurin yin kuka, shi ya sa na fi son rol ɗin tausayi – Sarauniya Zully

Daga IBRAHIM HAMISU

Zaliha Ishaq Abdullah da a ka fi sani da Sarauniya Zully, jaruma ce a Masana’antar Kannywood kuma ƴan jarida ce, a tattaunawar ta da Ibrahim Hamisu a Jos, za ku ji tarihinta, da kuma shekarun da ta yi a Kannywood, da kuma yadda take haɗa aikin jarida da kuma yin fim, ku biyo mu don jin yadda tattaunawar ta kasance:

MANHAJA: Za mu so ki gabatar mana da kanka ga masu karatunmu?

SARAUNIYA ZULLY: Sunana Zaliha Ishaq Abdallah (Sarauniya Zully).

Ko za ki ba mu taƙaitaccen tarihinki?
Ni ‘yar Jihar Adamawa ce. A can aka haife ni sannan muka dawo Jos da zama ni da iyayena. Na yi primary da secondary a Jos Baptist Academy sannan na yi school of Hygiene Kano na samu certificate, sannan na koma Kaduna na cigaba da makaranta a Jami’ar KASU. Yanzu ina matakin ƙarshe. A vangare ɗaya ina aiki da gidan talabijin na HIJRAH.

Ta yaya aka samu kai a masana’atar fim ta Kannywood?

Farko dai na fara ne da fassarar Indiya Hausa sannan ina waƙa kafin nan wani mawaqi mai suna Ahmad shanawa da ke garin Jos ya ja ra’ayina akan yin nidiyon wata wakar sa mai suna ‘Gaskiya’ na mai kunu da ƙosai shi ne farkon shiga ta bidiyo, bayan nan sai wata rana ana yin fim a Jos mai suna ‘Dogon Buri’ shi ma ansani na fito amatsayin matar Ali Nuhu to fa daga haka nafara, a taqaice kenan.

Masana’atar Kannywood ta na da faɗi ke a me ki ka fi ƙwarewa?

Gaskiya ina son na ga ina ‘acting’ ɗin tausayi domin ina da saurin yin kuka, hawaye tamkar teku.

A wacce shekara ki ka fara fitowa a fim?

Na fara Fim a shekarar 2018.

A wane fim ki ka fara fitowa?

Sunan fim ɗin ‘Dogon Buri’.

Ya zuwa yanzu za ki iya lissafa finafinan da ki ka yi?

Gaskiya suna da yawa ko zan lissafa dole zan manta wasu, amma ga kaɗan daga ciki: ‘Dogon Buri’, da ‘Ƙauran Mata’ da ‘Macen Soja’ da ‘Raees’, da ‘Duniyata’, da ‘Sadauki’ da kuma ‘Kabuwaya’.

Daga lokacin da ki ka fara zuwa yanzu waɗanne nasarori za ka iya cewa kin samu a harkar?

Alhamdu lillah ina ƙara godiya ga Allah sosai don babu abinda zan iya cewa ga masana’antar Kannywood sai godiya dan nasarori kan ba a magana.

Ko za ki lissafa mana kaɗan daga cikin nasarorin?

Alhamdu lillah narasa kam na samu sai godiya domin sanadin Kannywood ga shi an sanni kuma har ina iya taimaka wa mutane, misali marayu da gajiyayyu to ko wannan ma nasara ce da na samu a ciki domin ina da gidauniya ta da na yi wa suna Zully Foundation, amman ba na bayyana taimakon da nake yi sai dai ya bayyana kansa domin duk abinda ka ke yi don Allah to sai an sani dama baka faɗa ba.

Ƙalubale fa akwai ko babu?

Gaskiya ni ba na samun ƙalubale don bana shiga harkar da bai shafe niba.

Da wa ki ke koyi a Kannywood ?

Gaskiya dukkanin jarumin da yake da hali mai kyau to da shi ni nake koyi.

Waye maigidanki a Kannywood?

Ni gaskiya ‘Independent actress’ ce bana ƙarƙashin wani ‘company’, ko uban gida, domin ni ma ina da nawa kamfanin mai suna ZIA PRODUCTION NIG LTD. So ina dogaro da kaina.

Fitinafinai nawa ki ka shirya a ƙarƙashin kamfaninki?

Za su kai kamar guda biyar, amman guda 3 duk na gidan talabijin ne, wato HIJRAH TV.

Yaushe kik ka fara aiki da Hijira TV?


Na fara aiki da Hijrah TV ne shekara biyu da suka gabata.

Waɗanne shirye-shirye ki ke gabatarwa a Hijira TV?

Shirye-shiryen su ne: ‘Buhun Dariy’ da ‘Yara Manyan Gobe’ da ‘Taurari Tare da Zully’.

Ta yaya ki ke haɗa fim da aikin jarida?

Gaskiya ina amfani da ‘schedule’ shiyasa ba na samun matsala ko haɗa aiki a kaina.

Ko za ki iya tuna wani fim da ya baki wahala a wajen ɗauka?

Eh Sunan fim ɗin ‘Sadauki’ gaskiya na sha wahala sakamakon aikin a daji ne cikin duwatsu shiyasa nasha wahala.

Ganin irin yadda ake kwararowa a Masana’antar Kannywood musamman mata. Wacce shawara za ki bai wa masu sha’awar shiga?

To abinda zan iya cewa ga masu sha’awar fim ɗin Hausa idan ki ka shigo sana’arki ɗauke ta da mahimmanci sai ki ga Allah ya ba ki nasara, sannan matan aure masu son su kashe auren su su shiga fim don Allah ku zauna a gidan mazajenku domin mutuncin ƴaƴa mata gidan mijinsu muma da bamu yi ba Allah ya bamu mazaje na gari.

Menene burinki a masana’atar?

Burina shi ne naga ina aikin alheri a kowane lokaci don jama’a su daina aibata masana’antar mu ta Kannywood, ina jin daɗi idan na yi aikin alheri a ce wannan ƴar film ce saboda ina alfahari da sana’ata.

Ya batun aure fa?

Ban taɓa yin aure ba, amman ina addu’a Allah ya ba ni miji mai tausayi sannan na gari.

Idan ki ka samu miji yanzu za ki ajiye fim ɗin ki yi aure?

Insha Allah, ai in dai mutum ɗan aure ne, dole ka so aure, kuma mutuncin ƴa mace shi ne gidan miji.

Mun gode.

Ni ma na gode.