NATO—Makamin neman babakere a duniya

DAGA AMINA XU

Babu buƙatar kasancewar ƙungiyar NATO a duniya bayan an kawo ƙarshen yaƙin cacar baka, abun da ya dace shi ne a tarwatsa ta kamar ƙungiyar Warsaw, domin kar ta zama wani makami mai ƙarfi ga Amurka na neman babakere a duniya.

Amurka ta sa kaimi ga NATO da ta ɗauki jerin matakai, ciki har da haɓaka zuwa gabashin Turai da ruruta wutar rikici tsakanin Rasha da Ukraine, da nufin matsa lamba kan Rasha, da ma ta da kiyaya tsakanin Turai da Rasha, kuma hakan zai bai wa Amurka ƙarin goyon baya, ta wannan hanya Amurka ta cimma burinta na ƙarfafa babakere a duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *