Duniya na buƙatar haɗin gwiwar daƙile manyan matsalolin da bil Adama ke fama da su

Daga SAMINU HASSAN

Ko shakka babu, duniya na fuskantar manyan ƙalubale daban daban, musamman a shekarun baya bayan nan, rikicin Rasha da Ukraine, da matakan da wasu ƙasashen yamma ke ɗauka na bin ra’ayin ƙashin kai, da ƙaƙƙaba takunkumi da wasu ƙasashen yamma ke yi ga wasu sassa, da tasirin sauyin yanayi, tare da cutar COVID-19 dake ƙara bazuwa a sassan ƙasashen duniya daban daban, dukkaninsu sun ƙara matsi ga tattalin arzikin duniya.

Masharhanta na ce, hauhawar farashin abinci, da makamashi, na ingiza ƙalubalen ƙamfar abinci da makamashi, ta yadda duniya ke tunkarar ƙamfar abinci mafi muni, tun bayan ƙalubalen ƙamfar abinci na shekarar 2007 zuwa 2008.

A nahiyar Afirka ga misali, farashin abinci ya ninka har sau 3 tun daga shekarar bara.

Kaza lika su ma ƙasashen Turai da dama na fuskantar wannan ƙalubale, inda maaunin farashin kayayyakin masarufi ko CPI a wasu daga cikin su ya ƙaru da kusan kaso 18 zuwa 20 bisa ɗari.

Tuni dai MƊƊ ta samar da tallafin abinci da darajarsa ta kai dala miliyan 97 ga ƙasashe 88, yayin da adadin yan gudun hijira ke ƙaruwa sakamakon rikicin Rasha da Ukraine.

Da yawa daga ƙasashen yamma, sun gaza sauke nauyin alƙawuran da suka ɗauka a tsawon lokaci, wato kashe kaso 0.7 bisa ɗari na daukacin kudaden shigar su a fannin tallafin samar da ci gaba, manufar da tun da farko ke da nufin bunƙasa ayyukan noma a ƙasashe masu tasowa, musamman na Afirka, da gabas ta tsakiya, ta yadda hakan zai wanzar da damar samar da isasshen abinci ga alummun ƙasashe masu tasowa.

Ko shakka babu, idan har ana da burin shawo kan waɗannan matsaloli, ya zama wajibi gwamnatoci su goyi baya ga kiraye-kirayen MƊƊ, na ingiza shigar da abinci, da takin zamani na ƙasashen Rasha da Belarus zuwa kasuwannin duniya, domin bunƙasa samar da hatsi, da kauce wa ƙaruwar matsalar kamfar abinci.

Tuni dai ƙasar Sin ta rungumi wannan manufa, inda a ɓangarenta, take dora muhimmanci ga tallafa wa raya noma a ƙasashe masu tasowa. Sin tana kuma ci gaba da ingiza ci gaban ginshikan tattalin arzikin duniya baki ɗaya.

A ɗaya hannun kuma, tun bayan da ƙasar Sin din ta daddale yarjejeniyar hana kwararar hamada ta MƊƊ, kawo yanzu tana ƙoƙarin bunƙasa aiwatar da wannan yarjejeniyar tare da haɗin gwiwar kasashen Afirka, inda take fatan cimma nasarar aiwatar da shirin gina ganuwar bishiyoyi ta Afirka, don kare kwararowar hamada, shirin da ake kira da Great Green Wall. Wannan ya zama wani mataki na ba da tabbaci ga burin da ake da shi na A guda tare a tsira tare.