Daga WAKILINMU
Hukumar Kula da Rarraba Wutar Lantarki ta Nijeriya (NERC), ta ƙara kuɗin wutar lantarki a ɓoye ba tare da sanin ‘yan ƙasa ba.
NERC ta yi haka ne ta hanyar bai wa kamfanonin rarraba lantarki umarnin su ƙara kuɗun wutar da suke bai wa jama’a.
Kamfanin Rarraba Lantarki na Abuja (AEDC), ya tabbatar da ƙarin farashin a saƙonsa da ya wallafa a shafinsa na Tiwita ranar Laraba.
Saƙon ya ce, “Barka dai, a sani cewa ƙarin farashin lantarki umarni ne daga NERC.”
Ya zuwa haɗa wannan labari, babu wani bayani a hukumance daga daga NERC kan batun.
