NYCN ta yi wa Sanata Adamu mubaya’a

Daga BASHIR ISAH

Majalisar Matasa ta Najeriya (NYCN), ta bayyana mubaya’arta ga Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, a matsayin wani mataki na tabbatar da APC ta tafi tare sa matasa a gwagwarmayar da take yi.

Hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da shugaban majalisar reshen Jihar Nasarawa, Jaafar Loko, ya fitar ranar Alhamis a Keffi.

Loko ya ce tabbatar da ana yi da matasa da inganta rayuwarsu na daga cikin muhimman abubuwan da majalisar ta sa a gaba don bunƙasa fannin dimokuraɗiyyar ƙasar nan.

Ya ce, “Bunƙasa matasa a siyasa da samar musu da damammaki masu alfanu haɗe da shigar da su harkokin siyasa da tattalin arzikin ƙasa na daga cikin hanyoyin da za a bi don kyautata rayuwar matasa.”

Don haka ya ce, damawa da matasa cikin harkokin siyasa abu ne da bai kamata a yi watsi da shi ba.

Daga nan, Loko ya nuna cewa tun ba yau ba Shugaban APC na ƙasa ya saba tafiya da mata tun a zamanin da yake Gwamnan Jihar Nasarawa.

Kazalika, ya nuna godiyar majalisar ga Sanata Adamu bisa naɗa ɗaya daga cikin mambobinta, Muhammad Lawal, a matsayin Mai Taimaka Masa Kan Sabbin Kafafen Yaɗa Labarai.

“Naɗa Lawal a wannan muƙamin ya ƙara bai wa matasan Nasarawa ƙwarin gwiwa wajen ci gaba da mara wa APC baya,” inji Loko.