Har yau akwai masu kai marubuta wuta a kalamansu – Ruqayya Ibrahim Lawal

“Ban cika damuwa da rashin sharhin masu karatu ta”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Marubuta mutane ne masu ɗimbin baiwa, waɗanda akasarin su za ka tarar baiwarsu ba ta tsaya kan ƙirƙirar labari kaɗai ba, suna da wasu hikimomi da suke cin abinci da su, ko kuma sana’o’in dogaro da kai na yau da kullum. Ruqayya Ibrahim Lawal da aka fi sani da Ummu Inteesar daga Jihar Sakkwato, na daga cikin irin waɗannan marubuta ‘yan baiwa da za a iya ce musu ýan komai da ruwanku, don kuwa ba ta tsaya kan harkar rubuce-rubuce kaɗai ba, har ma da wasu sana’o’i da ta ke yi. Da dama za su yi mamakin jin cewa Ummu Inteesar marubuciyar waƙoƙi ce, ýar kasuwa ce, ýar jarida, malamar makaranta kuma mai sana’ar soye-soyen kayan ƙwalama. Sunan kamfaninta RUKY’S BAKERY ba ɓoyayye ba ne a Birnin Shaihu, inda ta ke koyar da harkar girke-girke da soye-soye da kuma kwangilar abinci a manyan taruka da buki. A ɓangaren rubutu kuwa, gwana ce wajen rubuta gajerun labarai bayan na littattafai da ta ke yi, tana kuma daga cikin marubuta mata da labaransu suka yi fice a gasar Hikayata ta BBC Hausa a shekarar 2021. Wakilin Blueprint Manhaja Abba Abubakar Yakubu, ya samu tattaunawa da wannan haziƙar marubuciya da ta ce babban burinta na rayuwa shi ne, ta yi wani abu da zai canza rayuwar wani, yadda duniya za ta yi alfahari da ita.

BLUEPRINT MANHAJA: Wacce ce Ummu Inteesar?
UMMU INTEESAR: Ni dai asalin sunana Ruƙayya Ibrahim Lawal, wacce a duniyar rubutu aka fi sani da Ummu Inteesar a duniyar sana’a kuma Ruky’s Bakery.

Shi wannan Ummu Inteesar ɗin kuma ina ya samo asali, kina da yara ne?
(Dariya) A’a, ni ban tava aure ba. Suna ne dai da na laƙaba wa kaina a lokacin da na fara rubutu, ganin sauran mata marubuta kowacce da irin nata laƙabin. Sannan kuma a makaranta an ce mana yin laƙabi na alkunya yana daga cikin sunnonin sahabban manzon Allah S.A.W, ba lallai sai mutum ya yi aure ba, shi ya sa na zaɓi sunan Ummu Inteesar, don sunan yana min daɗi. Akwai wasu daga cikin ƙawaye da ‘yan’uwana ma da yanzu suka saba kirana da sunan.

Yaya rayuwarki ta kasance a harkar karatu?
Na yi karatun firamare na a makarantar ‘Family Support Model’ da ke Sakkwato daga shekarar 2003 zuwa 2009. Na kuma je makarantar sakandire ta ýan mata ta Nana ‘Girls Secondary School’ daga shekarar 2010 zuwa 2012, bayan kammala karamar sakandire sai na koma makarantar Abdulrashid Adisa Raji duk a cikin garin Sakkwato daga 2013 zuwa 2015 inda na kammala karatuna na sakandire. Daga nan ban samu na ci gaba da karatuna ba, saboda rashin lafiyar mahaifiyata, sai a shekarar 2017 inda na samu damar shiga Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Umaru Ali Shinkafi, a nan na fara yin karatuna a matakin Diploma a ɓangaren ilimin gudanar da kasuwanci, kuma ni dama mai sha’awar harkokin kasuwanci ce. Sai dai Allah bai nufa na kammala ba karatuna a wannan makaranta ba saboda wasu dalilai.


Daga baya na sake shiga wata makarantar saboda nacin da na ke da shi don yin karatu, amma ba ɓangaren da naso a baya ba.
A shekarar 2019 na shiga Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Sakkwato, kuma in sha Allah a Ina gab da kammala karatun NCE ɗina. Alhamdulillah.

Gaya mana yadda ki ka fara samun kanki a matsayin marubuciya?
Da ma can tun ina ƙarama ni mai sha’awar rubuce-rubuce ce musamman na labari. Ina rubutawa na ajiye a littafi, na riƙa karantawa ƙannena da ƙawayena, ban taɓa tunanin cewa zan fara rubutu ba. Kwatsam rana ɗaya na ɗauki waya na fara kwafe rubutun daga littafina na tutturawa mutanena. Kuma na fara amsa sunan marubuciyar ne a watan Satumba na shekarar 2019, da littafina na farko, ‘Soyayyar Meerah’, kuma shi aka fara sani na da shi.

Daga lokacin da ki ka fara rubutu zuwa yanzu waɗanne ƙalubale ki ka fuskanta, game da iyaye, masu karatu da ýan’uwa marubuta?
Duk da cewa a rayuwa ba a rasa ƙalubale, amma dai har zuwa yanzu ban fuskanci wata matsala daga iyayena, ýan’uwa, marubuta ba. Ƙalubale ɗaya ne, shi ne yadda ƙawaye da sauran mutanen gari ba su fuskanci manufar rubutu ba, suke yi wa marubuta kuɗin goro, har wasu daga ciki sukan kai marubuci wuta kai tsaye.

Gaya mana adadin yawan rubutun da ki ka yi na littattafai?
Na rubuta littattafai a ƙalla guda bakwai da suka haɗa da ‘Soyayyar Meerah’, ‘Ýar Gantali’, ‘Rikicin Masoya’, ‘A Sanadin Kama’, ‘Halittar Allah Ce’, ‘Wata Anguwa’, ‘Wata Ƙawa’ (wanda shi na haɗa ka ne). Sai kuma gajerun labarai da na rubuta wanda kuma wasu na shiga gasa da su kamar haka; ‘Ƙuncin Rayuwa’, ‘Shahidah’, ‘Ɗa Kamar Kowa’, ‘Nana Aisha’, ‘A Ramadan’ da kuma ‘Kowa Ya Tuba Don Wuya’, sai ‘Ƙasar Kamoliya’.

Akwai kuma labarina mai suna ‘Ƙasata’, wanda na rubuta a matsayin ‘project’, yayin kammala makarantar horar da matasan marubuta ta Hausa Writers College da ake yi a yanar gizo, Yanzu haka an buga labarin a littafin haɗakar labaran ɗalibai da aka yi wa laƙabi da ‘Dukan Ruwa Ba Ya Hana Gwarje Amo’. Sannan na rubuta labarin ‘Sharri Kare Ne’, labarin da ya je mataki na biyu a zagayen ƙarshe a gasar Majalisar Marubuta ta farko.

Na kuma shiga gasar Hikayata wanda BBC Hausa ke shiryawa duk shekara, da labarin ‘Mataccen Alƙawari’, labarin da ya yi nasarar zuwa a cikin jerin labarai 25 aka fara tacewa a cikin jerin labaran da suka shiga gasar 2021. Banda waɗansu kuma da na shiga gasannin da ake kan tantancewa yanzu haka.

Na ji cewa, kin yi karatu a Kwalejin Marubuta Hausa ta ‘online’, wanne darasi za ki ce kin koya da ya ƙara inganta rubutunki?
Na samu cigaba ta fannoni da dama a rubutuna ta dalilin wannan makaranta. Ka ga a nan na koyi rubutun fim wanda na ke hango ba zai ba ni wuya ba idan na ce zan gwada.

Wanne ɓangare ki ka fi mayar da hankali a kansa a rubuce-rubucenki?
Ɓangaren zamantakewa da mu’amala ta yau da kullum, musamman abin da ya shafi zaman gida da iyali.

Yaya mu’amalar ki ta ke da masu bibiyar littattafanki, wanne abu ne suka yi miki da ya tsaya miki a rai, na farin ciki ko akasin haka?
Mu’amalata da masu bibiyar littattafaina kyakkyawar mu’amala ce mai cike da kyautatawa. Ƙaunar da suke nuna mini, yadda wasu kuma suka mayar da ni tamkar ‘yar’uwa shi ne, abin da ya fi tsaya mini a rai.

Yaya ki ke ji a ranki idan masu bibiyar littattafanki, ba su miki sharhin da ki ke tsammani daga gare su ba?
Gaskiya kam abin ba daɗi. Domin za ka ga kana ta ƙoƙari don al’umma, amma su kuma sai su gagara yi maka sharhi ko da layi biyu ne, amma hakan bai cika damuna ba, tunda ina yi ne da nufin faɗakarwa. Fatana kawai saƙon ya isa kunnen waɗanda na yi domin su.

Ana cewa marubutan ‘online’ kara zube suke fitar da littafinsu babu wani abu da suke samu, ke kin taɓa samun wani alheri ta dalilin rubutu?
E to, ni ban goyi bayan wannan zancen ba. Duk da kasancewar akwai tsare-tsaren da ya kamata a ce ana bi, don inganta kasuwancin rubutun ‘online’, amma ƙoƙarin marubuta ba ya tashi a banza. Domin ni na samu alkhairai sosai a dalilin rubutun ‘online’. Kamar Kyautar kuɗaɗe daga masu karantu da kuɗin littafin siyarwa. Rubutun ‘online’ ya yi mini komai!

Kin taɓa samun kyauta daga Gasar Gajeren Labari da ki ka ce kina shiga?
Tabbas ina shiga, na tava lashe wata gasa da wata ƙungiyar marubuta ta Tambari Writers ta saka, kuma labarina mai suna ‘Ƙuncin Rayuwa’, shi ne ya zo mataki na uku, har ma kuma an ba ni kyauta ta musamman.

Wacce ƙungiyar marubuta ki ke, kuma wanne cigaba ki ke samu daga gareta?
Ni mamba ce a ƙungiyar Arewa Writers Association, kuma ina samun cigaba sosai a dalilinta, zan iya cewa kusan duk abin da na samu a rubutun ‘online’ silar wannan ƙungiyar ne. Ina matuƙar alfahari da ita.

Ta yaya marubutan ‘online’ za su kawo sauyi ga yadda suke rubuce-rubucensu?
Ta hanyar jajircewa da inganta rubutunsu, tsananta bincike kafin fara rubutu, samar da tsaro ga littattafansu.

Me ki ke nufi da samar da tsaro ga littattafansu?
Ya kamata marubutan yanar gizo su ƙirƙiro wata hanya da za su bai wa littattafansu kariya daga masu satar fasaha, ko ta hanyar saka lambobin sirri wato ‘code’ su rufe littafinsu da suka sa a ‘document’ ko ma dai duk wani abu da zai kare littafin daga faɗawa hannun masu satar fasaha.

Menene ra’ayinki game da ƙoƙarin da wasu marubuta ke yi na ƙirƙiro da, wata Manhaja da za a riƙa tallata littafi da cinikinsa, irin su Arewa Books da Okada Books?
Gaskiya sun yi tunani mai kyau, kuma sun zo da cigaba mai ma’ana. Ina fatan wannan ƙoƙarin nasu ya ɗore kuma ya amfani waɗanda aka yi domin su wato mu marubutan adabi.

Bangon littafin ‘Halittar Allah Ce’

Bayan rubutu, wacce harka ta kasuwanci, aiki ko sana’a ki ke yi?
A baya na gaya maka Ina da sha’awar harkokin kasuwanci sosai, to, ban da wannan Ina kuma da sha’awar yin girke-girke, don yanzu haka ma Ina da kamfanina da nake harkar soye-soyen kayan ƙwalama wato Ruky’s Bakery.

Ina sana’ar sayar da kayan sanyi (drinks) iri daban daban. Da kuma kayan ƙwalama irin na soye-soye kamar su kek ɗin bukin aure ko na murnar zagayowar ranar haihuwa, cin cin, Samosa da sauransu. Ina fatan wata rana Ruky’s Bakery ya bunƙasa kuma ya shahara.
Sannan na gaya maka Ina karatun malamanta wato NCE, sannan Ina taɓa aikin jarida a zaurukan sada zumunta na soshiyal midiya. Ina tare da Ranɗawa Media Concept masu ‘Online Radio’. Da kuma masu mujallar Managarciya.

To, wacce ɓoyayyiyar baiwa ki ke da ita, wadda ba kowa ya sani ba?
(Dariya) Waƙa, ita ce abar da na fi sha’awa kuma nake yawan yi don nishaɗi. Duk da ban cika zama don sauraren waƙoƙi ba. Ina da wani littafi na kundin waƙoƙi da na tava rubutawa Ina ƙarama, sai dai akasari waƙoƙi ne na yabo wato ƙasidu ne irin na Islamiyya. Amma ba situdiyo nake shiga a buga min ba, amma a gida nake rera wa don nishaɗi.

Gaya mana lokacin da ki ka fi sha’awar yin rubutu?
Na fi sha’awar yin rubutu a lokacin da ba hayaniya a kusa da ni, shi ya sa na fi jin daɗin yin rubutu da tsakiyar dare.

Wacce karin magana ce take tasiri a rayuwarki?
Zakaran da Allah ya nufa da cara, ko ana muzuru ana shaho sai ya yi.
Sannan, ɗan hakin da ka raina shi ke tsole ma ido.

Mun gode.
Ni ma na gode.