Rashawa: ICPC ta gano sama da biliyan N1 a gidan Buratai

Daga BASHIR ISAH

Tsohon Babban Hafsan Hafsoshi, Tukur Buratai, ya sake samun kansa cikin wata sabuwar badaƙalar rashawa bayan da hukumar yaƙi da rashawa ta ICPC ta gano maƙudan kuɗaɗe sama da biliyan N1.89 ɓoye cikin wani gida a Abuja da aka ce mallakar Buratai ɗin ne.

An rawaito cewa, jami’an ICPC sun yi wa gidan da ke yankin Wuse dirar mikiya ne baya ne biyo bayan bayanan sirrin da hukumar ta samu.

Jaridar Peoples Gazette ta ce, da aka nemi jin ta bakinsa kan batun, Buratai ya ce ICPC ba ta da izinin binciken gidansa.

Buratai wanda shi ne jakadan Nijeriya a Jamhuriyar Benin ya ce, “Babu wanda ya samu izinin binciken gidana,” ya faɗi hakan ne a wani kiran waya da aka yi masa.

Sai dai, bai tabbatar da binciken da aka yi a gidan nasa ba balle kuma tabbatar da kuɗaɗen da aka ce an gano a gidan.

Sahara Reporters ta ruwaito wata majiya na cewa, “A ranar Alhamis ta makon jiya, jami’an hukumar ICPC sun yi dirar mikiya a wani gida da ke yankin Wuse a Abuja, daura da Buɗaɗɗiyar Jami’ar Nijeriya inda suka cafke wani mai suna Kabiru Salisu bayan da suka gano tsabar kuɗi har miliyan N850 a cikin gidan.

“Mutumin ya ce kuɗin mallakar Tukur Buratai ne wanda a wannan lokaci yana ƙasar Kwatano.

“Jami’an ICPC sun sake ɗaukar Salisu zuwa wani ofis inda a nan aka sake gano tsabar biliyan N1 da wasu motoci masu sulke ƙirar BMW da G-Wagon waɗanda kuɗinsu ya kai miliyan N450.”

Idan dai za a iya tunawa, ko a 2016 Buratai ya samu kansa cikin badaƙalar rashawa game da kadarorin da ya mallaka a Dubai.

Buratai ya riƙe muƙamin Babban Hafsan Hafsoshi ne daga 2015 zuwa 2021.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *