Daga AMINA YUSUF ALI
Barkanmu da sake haɗuwa. Sannunku da jimirin karatun jaridarku mai farin jini, Manhaja. Fatan an yi zaɓe lafiya. Allah ya sa jagororin da muka zaɓa su zame wa qasar nan alkhair bakiɗaya.
A wannan mako muna tafe da bayani a game da yadda ma’aurata za su buɗe ƙofar fahimtar juna a tsakaninsu. Wannan matsala ta rashin fahimtar juna duk da yadda ake raina ta, idan ta yi kaka-gida a zaman aure, tana samar da babbar matsala har ma da rabuwa.
Ba lallai ne mai karatu ya yarda da ni ba idan na ce matsalar rashin fahimta tana daga cikin manyan dalilan da ake samun matsaloli bayan aure ba. Sai ka ga an ƙulla aure irin na soyayya, amma daga zarar an tare, sai a yi ta samun savanin da ba a san dalilinsa ba. Sai mutane su yi ta mamaki. Abin ma fa har ya zama ruwan dare. Dole bayan aure sai an yi ta samun saɓani. Wasu sun ma mayar da abin dole wai idan aka yi aure sai an samu haka.
Amma ba wai rashin dace ne kuka yi na samun abokan zama na gari ba ne, ba kuma soyayyarku ce ko girmamawar dake tsakaninku ce ta yi sanyi ba. Ba kuma wasu matan mijinki yake hange ba kamar yadda shaiɗan zai ta raɗa miki. Wani lokacin kawai rashin fahimtar juna ce ta yi yawa. Kuma kun ƙi yarda ku fuskanci matsalar ko ku zauna ku tattauna a kai.
Kafin a yi aure, da farkon zaman aure, kowa yana ƙoƙarin fito da halayensa da za su fi daɗaɗawa abokin zamansa. Amma idan zama ya yi zama, za a gaji da hakan a fito da halayen gaskiya. Hakan shi yake yamutsa hazon zamantakewar Ango da Amarya.
A ƙasar Hausa ma’aurata kan kai matsalarsu ga magabata koyaushe aka samu saɓani. Amma da za ku zauna ku fahimci juna, ko a tsttauna a gano matsalar, da ya fi.
Amma sai a dinga yanke wa juna hukunci cikin zargi da rashin fahimta. Wani abin ma da za a kawar da zargi da girman kai a zauna a tattauna, sai a ga ma duk haushin juna ake ji a iska. Ko a yi ta ƙullatar juna a kan abinda ma mutum bai san ya aikata ba. Wani lokacin sai an yi musu ko cacar baki sannan ɗaya zai gane ainahin ma laifin da ya yi har ake ƙullatarsa. To me karatu, Hausawa dai sun ce rigakafi ya fi magani. Don haka sai a tari matsalar da wuri.
Shi fahimtar juna shi wani mabuɗi ne na samar da shaƙuwa da kusanci da yarda da juna da ɗorewa a zaman aure. Sannan kuma za a kiyaye faruwar saɓani a nan gaba, tunda an riga an gano bakin zaren.
Alamomin dake nuna zaman aure yana cikin gararin rashin fahimtar juna sun haɗa da:
- Nuna fushi cikin dabara: Wasu ma’auratan idan ransu ya ɓaci da abokin zamansu sukan yi ƙoƙarin nuna ransu ya vaci ba tare da sun bayyana musu ainihin abinda ya faru ba domin a tattauna a samu maslaha. Misali mijin da yake ƙullatar matarsa a kan wani laifi da yake zargi ta yi masa. Ya daina mata magana ko kuma ya daina cin abincinta har sai ya gaji ya sakko ba tare da ya gaya mata laifinta ba. Ko kuma a dinga ya da wa juna maganganu da habaici maimakon a tunkari matsalar a tattauna a kai.
- Ƙullatar mutum da yin shiru a kan matsalar. A ƙasar Hausa ana yawan ce wa mace ta yi haƙuri a kan duk girman matsalar da taso a gidanta na aure. Sai ka ga duk abinda namiji ya yi mata ba ta iya faɗa masa ko neman bayani sai ta shanye kawai a cigaba a haka. Wata kuma ta riga ta san ba ta da wani ƙarfi ko iko a kansa. Duk abinda ya yi kawai sai ta rabu da shi. Haka ma wani namijin yake mai zurfin ciki mai gudun fitina da iyali. Amma abinda ba su sani ba, shi wannan kau da kai da suke yi a kan laifukan abokan zama a zuciyarsu fa yana nan danƙare, a baki ne kawai ba su furta ba. Sai ka ga sun ƙullaci juna har ma hakan ya haifar da gaba ko kuma wata gingimemiyar matsalar a gaba da ma za su kasa shawo kanta.
- Yin kausasan maganganu ga juna da ɗaga murya, tare da muhawara mai zafi da nuna ɗan yatsa ga juna daga zarar wani musu ya haɗa ku. Shi ma alama ce ta rashin fahimtar juna a zaman aure. Domin alama ce da take nuna waɗancan matsalolin da kuke ta kauce musu gudun kada a yi tashin hankali da juna suna nan suna binne cikin zuciyoyinku kuma suna nan suna barazanar haifar da ƙatuwar matsalar da za ta iya rusa auren naku.
- Zargi: Rashin fahimtar mutum yana sa ka yi ta zarginsa a kan abubuwan da yake aikatawa. Haka fahimta tana haifar da yarda. Idan zargi ya yi yawa a tsakanin ma’aurata, kuma ba wai aikata wani abu ake yi na zahiri da zai iya haifar da zargin ba, to a bincika akwai rashin fahimta. Zargi yana kai wa duk inda zai kai ganin ya rusa aure.
Matakan da za a bi don samar da fahimtar juna suna da yawa. Sun haɗa da:
- Ba da damar tattaunawa a tsakaninku. Kada ku hana abokan zamanku damar tattaunawa da ku. Domin a irin wannan tattaunawar ne ake iya fahimtar juna da warware matsalolin da suke akwai. Kada ka ƙunshe abinda yake ranka ko yake ranki. Idan wani yana zargin wani da wani abu a ba shi dama ya yi magana don bayyana manufarsa. Hakan zai ƙara muku shaƙuwa da yarda da juna.
- Na biyu, ka fito da abinda yake zuciyarka. ka ce za ka karanci aboki/abokiyar zama. In dai fahimtar kake buƙata, ba hasashe ko zargi ba, to kada ka ce za ka karanci mutum ka gano abinda yake zuciyarsa. Hakan ma barazana ce ga zaman lafiyarku. Miji ko matarku ba littafi ba ne, ballantana ku ce za ku karance su ku fahimce su. Kuma su ma ajizai ne kamar kowanne ɗan’adam. Don haka a yi musu uzuri kuma a tambaye su cikin hikima a kan wani abin dauke aikatawa. Ko kuma a dinga tuntuɓarsu don jin ra’ayinsu a kan wasu abubuwan da kai kuma kake aikatawa.
- Kada a tunkari juna cikin fushi. A yi magana ta fahimta duk lokacin da aka samu savani. Yanke hukunci cikin fushi yana kawo da-na-sani. Tunkarar juna cikin fushi ba ta da wani alfanu. Shirun ma ya fi ta amfani. Domin muhawara ce zazzafa za ta faru sannan daga ƙarshe a yi cacar baki a ƙare baram-baram.
- Zaɓar lokacin da ya dace domin tattaunawa da abokin zama. Ma’aurata su suka fi kowa sanin junansu da lokacin da suke cikin nishaɗi. Wani lokacin cin abinci ne, wani sai da daddare sawu ya ɗauke da sauransu. To zaɓen lokacin da ya dace yana sa a samu abinda ake so. Yi musu magana a lokacin da bai dace ba shi ma yana ƙara ta’azara matsalar. Sanar da su cewa kana son magana da su shi ma yana ƙara sa wa a samu sauƙin rashin fahimta. Za su shirya wa lokacin ba kamar a tunkare su gaba-gaɗi ba.
- Kada a dinga yawaita zargi da ɗora laifi kan mutum guda. Zaman aure na mutane biyu. Kada wani ya ɗauka dole shi fa ba ya laifi ɗaya abokin zaman nasa ke da matsala. Sam! Don haka idan kana duba taka matsalar za a fi samun maslaha. Idan an samu saɓani kada ka ce kullum ba ki da aiki sai yin kaza. Gara ka mai da hankali a kan abinda ta yi maka a lokacin, sai a fahimci juna. Daga ka fara ƙorafin cewa ba ta da aiki sai kaza, to za ta ɗauka tuhumarta ka zo yi ka ƙure ta ba gyara kake so ba. Don haka ita ma fa ba za ta taɓa saurarenka ko fahimtarka ba. Sai ita ma ta dinga ƙoƙarin tuno tsofaffin laifukanka, daga nan komai zai cakuɗe ya zama matsala.
- Saurarar juna: Wani lokacin yayin tattaunawa sai ka ga ma’aurata sun toshe kunne sun qi saurarar abinda ɗayan yake faɗa. Kowa ƙoƙari yake yi a ji maganarsa. Hakan sam ba ya kawo fahimta sai dai ma ya qara cakuɗa lamurra. Abin ya zama muhawara kowa yana so ya zama zakaran da zai cinye wannan muhawara ba ma wai ta fahimtar juna ake yi ba. Amma da za ku tsaya kowa ya saurari ɗanuwansa da idon basira, ko da ra’ayinku bai zo ɗaya ba, amma a ƙalla kun fahinci halin da kowanne yake ciki. Ba gasa ba ce.
- Haƙuri: Ya zama wajibi ku haƙura da wani hali ko halayya ta abokin zama. Akwai halin da mutum ba zai canza ba. Saboda ba zai iya ba ko kuma ajizan in ɗan adam. Dole ɗaya daga ciki ya haƙura ya sadaukar da kansa. Tunda dai ba kai ka haife su ko ka halicce su ba. Maimakon a yi ta jayayya a kan abu guda yana kawo muku matsala a Aman aure. Misali namiji ba ya son mai aiki a gidansa. Amma duba da yanayin aikinsa da na matarsa sai ya sadaukar da kansa ya haƙura kada a yi ta samun savani.
- Sanar da juna abubuwa don gudun zargi: Ita zuciyar mutum da ma akwai ta da zargi. Musamman a zaman aure tunda shaiɗan da ma yana gaba da shi, zai ta ƙoƙarin ganin yadda zai kawo cikas ta hanyar sanya zargi da wasi-wasi a tsakaninku. Irin haka namiji idan ya kai dare a waje, duk da ba haƙƙinta ba ne, zai iya ce wa matarsa ga inda ya tsaya. Haka ita ma matar idan ya ba ta kuɗi don sayen wani abu idan abin ya ƙara tsada ko ta yi ciko za ta iya sanar da shi don gudun gaba kada a samu matsala. Irin waɗannan ƙananan abubuwa suna nan birjik a gidan aure. Rashin faɗar ne kawai fa yake haifar da shi. Da an faɗa kafin abin ya faru da sai an kawar da rashin fahimta sosai.
- Bayyana abubuwan da ake so da waɗanda ba a so: Yana daga cikin abubuwan da suke kawar da rashin fahimta a zaman aure, a bayyana wa juna abinda ake so da wanda ba a so. Yawanci ma fa abinda ke kawo rashin fahimtar shi ne, rashin sanin abinda aboki ko abokiyar zama ba sa so. Wani vata ran fa ba da gan-gan ake yi maka ba, cikin rashin sani ne. Don haka bayyana wa abokin zama ra’ayinka yana da matuƙar muhimmanci. Kuma zai rage rashin fahimta sosai.
Za mu cigaba a mako mai zuwa ina rai ya kai.