Rijiyoyin burtsatse da Sin ta gina sun taimaka wajen kawo ƙarshen matsalar rashin ruwa mai tsafta a Rwanda

Daga CMG HAUSA

A baya, dubban mazaunan gabashin Rwanda ne suka yi fama da rashin tsaftataccen ruwan sha saboda matsalar fari.

Misali, a yankin Rwinkwavu na gundumar Kayonza dake lardin gabashi, mazauna sai sun yi tafiya mai nisa, kafin su samu ruwa mai tsafta.

Sai dai yanzu, wannan matsalar ta zama tarihi, bayan ayyukan ginin rijiyoyin burtsatsai 200 da ƙasar Sin ta samar da kudin aiwatarwa, domin kawo ƙarshen matsalar rashin ruwa a lardin. A baya-bayan nan ne aka kammala aikin tare da ƙaddamar da shi, inda mutane 110,000 ke amfana.

Mazauna a gundunmomi daban daban na lardin, sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, yanzu ba su da wata matsala ta samun ruwa a yankunansu.

A yanzu, mazaunan Rwinkwavu na gundumar Kayonza dake lardin gabashi na ƙasar Rwanda, suna samun ruwa mai tsafta daga rijiyar burtsatsai dake amfanin da makamashin hasken rana.

Fassarawa: Fa’iza Mustapha