Duniya na buƙatar sa ido kan ‘yan siyasar Japan dake neman ɗaukar matakan soji

Daga CMG HAUSA

A bana ake cika shekaru 75 da aiwatar da kundin tsarin zaman lafiya na Japan. Sai dai, wasu jerin abubuwan da ‘yan siyasar ƙasar ke yi sun nuna yadda suke kaucewa hanyar zaman lafiya da neman yi wa kundin tsarin katsalandan ta hanyar ruruta cewa ƙasar na fuskantar barazana daga waje, a yunkurinsu na neman Japan ta kafa rundunarta na tsaron ƙasa da samun damar tada yaki. Ya kamata ƙasa da ƙasa su kwan da sanin cewa wasu ‘yan siyasar Japan na neman aiwatar da matakan soji.

Mai fassarawa: Fa’iza daga CMG Hausa