Bayyana ra’ayin takara: ’Yan Nijeriya na kira ga Buhari da ya tsige gwamnan CBN

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

An buƙaci shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da ya kori gwamnan babban bankin Nijeriya, Godwin Emefiele daga muƙaminsa kan nuna ra’ayinsa na tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023.

Idan za a iya tuna cewa, Emefiele wanda ya sha musanta burin zama shugaban Nijeriya a 2023, ya zaɓi fom ɗin tsayawa takara a ranar Juma’a.

Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnan babban bankin na CBN ya karɓi fom ɗin Naira miliyan 100 daga hannun sakataren jam’iyyar na ƙasa (ICC) da ke Abuja.

’Yan Nijeriya da suka mayar da martani kan wannan lamari sun ce ba bisa ƙa’ida ba ne a ce Gwamna CBN mai ci ya yi siyasa, don haka ya kamata ya yi murabus ko kuma a tilasta masa yin murabus.

Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu ya ce, Emefiele ba zai iya taka rawar gani a siyasar bangaranci ba kuma ya riƙe muƙamin gwamnan CBN.

Har ila yau, wani lauya mai kare haƙƙin ɗan Adam, Festus Ogun, ya ce, matakin da gwamnan CBN ta ɗauka na tsayawa takarar shugaban ƙasa abu ne da ya dace.

Ya bayyana cewa, gwamnan na daya daga cikin waɗanda ke cikin kwamitin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da ke da hannu wajen yin hakan.

Fadar shugaban ƙasar dai ba ta fitar da wata sanarwa ba dangane da wannan lamari har zuwa lokacin da aka buga labarin.

A halin yanzu, babban taron jam’iyyar APC na musamman na zaɓen fidda gwanin takarar shugaban ƙasa zai gudana ne tsakanin ranar 30 ga watan Mayu zuwa 1 ga watan Yunin 2022.