Rundunar sojin saman Ƙasar Sin ta lashi takobin kare cikakken ‘yanci da yankunan ƙasar

Daga CMG HAUSA

Rundunar sojin saman ƙasar Sin, ta ce haƙƙi ne kan kowanne sojan samar ƙasar, ya kare yankuna da ikon ƙasarsa.

Kakakin rundunar Shen Jinke ne ya bayyana haka, yayin wani taron manema labarai da aka yi yau Lahadi.

A cewarsa, ƙudurin rundunar ne kare cikakken ‘yanci da yankunan ƙasar Sin, bisa jajircewa da dogaro da kai.

Fassarawar Fa’iza Mustapha