Tsadar fulawa da kayan haɗi: Gidajen burodi sun sanar da sabon farashinsu

Daga AMINA YUSUF ALI

Masu gidajen burodi a Nijeriya sun bayyana yadda farashin biredi zai tashi nan gaba. Sabon farashin ana sa ran zai fara daga ranar Litinin ɗin da ta gabata wato 25 ga Yuli, 2022.

Rahotanni sun bayyana cewa, a yanzu haka ma farashin biredin ya jima da tashi a wasu jihohin saboda abinda suka alaƙanta da tsadar fulawa da kayan haɗin burodin a Nijeriya.

Rahotanni daga jihar Kogi sun bayyana cewa, tuni masu gidajen burodin suka ƙara farashin biredin da ƙarin kaso 20% a kan tsohon farashinsa.

Wannan ƙarin farashin ya biyo bayan yakin aikin ƙasa bakiɗayan da Ƙungiyar masu gidajen biredi na ƙasa suka fara a ranar Larabar makon da ya gabata na tsahon kwanaki biyar. Sun yi yajin aikin suna neman gwamnatin Tarayya ta sa baki a kan tsawwalawar da ake musu a kan farashin kayan haɗin burodin.

Dalili na biyu na yin yajin aikin kuma shi ne, sun nemi gwamnati ta sawwaƙe musu matsanancin haraji har na kaso 15 da take cirewa a kan fulawa. Sannan a baya-bayan nan hukumar NAFDAC ta tilasta wasu gidajen burodi biyan tarar Naira 154, 000 saboda jinkiri wajen sabunta lasisin hukumar.

Shugaban ƙungiyar masu gidajen biredi a Nijeriya reshen jihar Kogi, Gabriel Bamidele-Adeniyi, ya bayyana wa majiyarmu cewa, wannan yakin aikin gasa burodi da suka yi sam kwalliya ba ta biya kuɗin sabulu ba. Domin Gwamnati sam ba ta ma bi ta kansu ko buƙatunsu da roƙonsa gare ta ba. Amma a cewar sa ko da gwamnati ba ta saurare su ba, a qalla ai sun isar da saƙo.

Sai dai a cewar Gabriel Bamidele-Adeniyi, suna baƙin cikin sanar da al’umma cewa, dole a ƙara farashin burodi daga yadda suke sayen sa a da.

Gabriel Bamidele-Adeniyi, ya bayyana misali da cewa, burodin da ake sayarwa a kan farashin Naira 200 yanzu zai koma Naira 240 zuwa Naira 250, burodin Naira 500 zai koma Naira 600, yayin da na Naira 600 zai koma Naira 750; Shi kuma na Naira 700, zai koma, Naira 880; shi kuma na Naira 800, zai zama Naira 980 zuwa Naira 1, 000.

A ƙarshe dai ya bayyana cewa, sam masu gidajen burodi ba su da laifi a kan wannan ƙarin farashi. Ba su da zaɓi ne, duba da yadda kayan haɗa burodin suka tashi. Inda ya yi kira ga gwamnati da ta sassauto musu da farashin yis, sukari, da fulawa. A cewar sa, ya kamata gwamnati ta ware kamfanoni uku kacal waɗanda su kaɗai za su samu lasisin shigo da waɗancan kayan haɗin.

Kodayake, su kuma ƙungiyar masu gidajen burodi reshen Abuja sun bayyana cewa, su ma sun so su shiga yajin aikin a makon da ya gabata amma dai ba su shiga ɗin ba. Sun gwammace su zauna da Gwamnati domin su samo mafita a lamarin. Sai dai kuma a cewar su, matakin da za su ɗauka kawai idan gwamnatin ta qi saurarensu shi ne, su ma daina gasa burodin gabaɗaya.

Shi ma a yayin zantawarsa da manema labarai, Thomas Odey, shugaban ƙungiyar masu burodi reshen jihar Kuros Ribas ya bayyana cewa, su ma jihar tasu ba ta bi sahun jihohin da suka yi yakin aikin ba. Amma sun ƙara farashin burodi su a gidajen burodi sannnan kuma sun rage yawan burodin da suke gasawa kullum, saboda gudun asara.

A cewar sa, rashin buga burodin zai iya jefa al’ummar cikin halin ƙaƙa-nika-yi domin abin masarufi ne da ya zame wa al’umma jiki. Kuma a cewar sa, idan al’umma suka kula ba burodin ne kawai ya ƙara kuɗin ba, dukkan sauran kayan abinci da na masarufi sun samu ƙarin farashi. Haka nan yaƙin Yukiren da Rasha shi ma ya yi matuƙar taimakaws wajen kawo tsadar fulawa.

Daga ƙarshe Mista Odey ya bayyana cewa, hanyar da za a shawo kan matsalar shi ne, a dinga amfani da rogo da dankali a cakuɗa da alkama wajen samar da fulawa. Amma a cewar sa, ƙasar nan ba ta noma isasshen rogo da dankali da zai wadaci buƙatar alkamar ƙasar.