Sakkwatawa na kokawa kan ramukan titina a wasu manyan hanyoyin birnin

…Tuni muka soma magance matsalar, cewar Hukumar Tsara Birnin Sakkwato

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato

Wasu masu amfani da ababen hawa a Jihar Sakkwato sun yi kira ga mahukunta da su duba hanyoyin gyara titina dama shatale-shatalen dake ƙwaryar birnin Sakkwaton, lamarin da suka ce rashin gyaran na iya kai ga rasa rayuka da ma dukiyoyin al’umma.

Kiran nasu dai na zuwa ne a daidai lokacin da titinan dake ƙwaryar birnin jihar ke fama da matsalar fashewar, wanda masu amfani da ababen hawan musamman masu sana’ar kabu-kabu ke cewa hakan na iya kawo tsaiko ga tattalin arzikinsu.

Titinan dake fama da matsalar dai sun haɗa da na tsohuwar kasuwa dake kan titin Aliyu Jodi da kuma na Bello Way, wanda ya haɗa titin Maituta da na Gidan Dare, da shatale-tale mai ruwa, Bye Pass na gabashin Sakkwato da dai sauransu.

Wani ɓangaren hanyar Sakkwato

A lokacin da wakilinmu ya tuntuɓi mataimaki na musamman ga Gwamna Aminu Waziri a hukumar tsara Birnin Sakkwato da kewaye Sidi Aliyu Lamido ya ce suna da masaniyar halin da hanyoyin suke ciki wanda tuni suka soma gyaran wasu hanyoyin.

“To gyaran titi ko ko yanayin da titi ke shiga cikin lokacin damina ba yanayi ne na ƙorafi ba, yanayi ne na kai me ka yi? Ni me na yi? Shi me ya yi? kuma me ake yi, illa kawai Alhamdulillahi a mataki na hukumance Allah ya sani muna bakin gwargwadon mu mu sauke namu haƙƙi wanda Allah ya ɗora mana.

Gyaran titi wani nau’i ne na ibada, ibada ce ba wai ma aiki ba ne, Alhamdulillahi kowa ya gani Maigirma Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya ɗauke nashi haƙƙi bisa ga mu ƙwarin gwiwar da ya ke ba mu na mu yi gyaran titina, kuma ya ɗauke na shi haƙƙi bisa ga titunan da ya ke yi, da gadoji da dukkanin abubuwan da a ke yi, illa kawai abinda muke fata Allah ya sa mai ni’ima da hali da yawancin rai ne ya sa ya ci amfani abinda ya yi wa jihar Soakkwato.”

A cewarsa hukumar tasu ta gyara titin Binji Pharmacy da na Amadu Bello Way da na Emir Yahaya da can na Gobirawa, tsakanin aikin da muka yi jiya da yau mun samu baiwa ta Ubangiji, cikin iyawar Ubangiji mun gyara titinan, kuma in sha Allahu Rabbi muna sa ran daga nan zuwa juma’a idan Allah ya bai wa mutane dama suka bi saman waɗannan titunan suka daddale wannan gyaran da muka yi to in sha Allahu za mu je mu sa kwalta mutane su ci gaba da amfani da su, ƙorafi da ka ce an yi ni mamaki ka ke yi yadda ake ƙorafi domin ba abin ƙorafi ba ne abin faɗakarwa ne don kowa ya sani wannan ma’aikata dama ma’aikatan nan da ke da alaƙa da mu da kuma ko wane lokaci suna irin waɗannan ayyuka,” inji shi.

A cewarsa aikin da suka soma za su yi ƙoƙari ne na game ƙwaryar birnin Sakkwato.

“Idan gwamna zai ba mu aiki cewa ya ke yi muje mu yi gaba ɗaya be taɓa ce mana mu yi mu tsallake ba, kamar yadda na gayama lokacin damina lokaci ne da cututtukan da ke cikin tituna suke fitowa.”

Sidi Aliyu Lamido hakama ya bayyana cewa daman duk kan lokacin damina irin wannan ana samun matsalar wanda ya ce hukumar su da gwamnatin Aminu Waziri Tambuwal na yin duk ƙoƙarin su wajen kawar da matsalar a duk kan titunan dake ƙwaryar birnin Sakkwato.

Haka ma ya qara da cewa sakamakon ƙarin yawan mutane ne dama rashin iya tuƙi na wasu ke Sakkwato ke samu ke haifar da yawan lalacewar titunan.

“Galibin titinan sun kuma yanayin nau’in kwaltar da ake amfani da ‘ita da kuma cikon da ake amfani da shi, kwalta tana da rayuwa, idan lokacin mutuwarta ya yi dole ta mutu, kamar ɗan Adam ne shi ma, sanadiyyar daɗewar da ta yi, sannan kuma tana samun karamcin ya zama a kasheta kuma, sanadiyyar ganganci, na tuqin ganganci da ake yi da yawan haɗarin da ake samu yana cikin abubuwa da ke kawo lalacewar titi ko mi gyaran da ka yi masa, na biyu lodi da ake yi wa motoci manyan motoci yana kawo lalacewar titi mota ya kamata ta ɗauki tom talatin ko ashirin amma sai ka ga ansa mata sittin.

Rami a hanyar Sakkwato

Daga nan sai ya yi kira ga ƙungiyoyi da ɗaiɗaikun mutane dake son cigaban Jihar Sakkwato da su cigaba da haɗa guiwa da hukumar ta yadda za a shawo kan matsalar fashewar.

“Kira na ga al’umma su zama masu taimaka wa gwamnati, domin gwamnati al’umma sune ita , taimakon da suke iya yi wanda ya ga abinda ya cutar da al’umma to shi hana, kamar wanda ya ga wani zai gine titi ko wanda ya ga wani ya yi lodin da ya wuce wuri, ko wanda ya ga titin ma ya lalace kila abinda ya ke buƙata a sa dutse a rufe ko tsakuwa don Allah idan a kwaita kusa ko ta gwamnati ce ko tashi ya ɗauko ya sa, domin hannu ɗaya ba ya ɗaukar ɗaki, amma Alhamdulillahi zan yi amfani da wannan damar in yaba wa waɗanda ke ganin waɗannan ga illoli suna gayama mana, har ku kan ku ‘yan jarida, muna jin daɗi ƙwarai da gaske don haka duk lokacin da aka nememu kan tattaunawa kan wannan matsalar ba mu tava ƙasa a gwiwa ba mukan zo mu bayar da shawara,” inji shi.