Matashi ya kashe kishiyar babarsa, ya karya babansa a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina

Wani matashi mai suna Najib Shehu Umar, ɗalibi a Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ta ke Dutsinma (FUDMA) ya kashe kishiyar mahaifiyar shi daga bisani ya kuma karya kafar mahaifinsa a Katsina.

Kamar yadda Manhaja ta samu, Najib ya sha furta cewar sai ya kashe Hajiya Hasiya Galadima wadda ita ce kishiyar mahaifiyar ta sa.

Yana zargin ita ce tai sanadiyyar raba auren mahaifiyarsa da mahaifinsa. Najib ya shiga ɗakin girki, inda ya ɗauko tavarya ya shigo inda marigayiyar ke zaune tare da ‘yarta da kuma wasu mutane daban bai yi wata-wata ba ya kulle ɗakin.

”Kin san na ɗauki alƙawarin wata rana sai na kashe ki idan za ki iya tunawa, to yau zan kashe,” inji shi.

Kafin ka ce kwabo Najib ya kwaɗa wa marigayiyar taɓarya a kai har sau biyu nan take ta faɗi a  sume.

Bayan da ta suma ya dawo ɗakinta ya tarar ba ta rasu ba, ya kuma ƙara buga mata taɓarya sai da ya tabbatar da ba ta motsi kamar yadda majiyar mu ta tabbatar mana.

Mahaifin Najib na ɗaki koda ya ji ƙara ta yi yawa sai ya fito don gane ma idonsa abun da ke faruwa a ƙoƙarin kare ‘yar uwar ɗan nasa sai matashin ya buga wa mahaifin nasa tavarya a ƙafa shi ma ya faɗi ƙasa sume saboda karaya da ya samu a ƙafa da hannu ita kuma ta ruga maƙota don neman taimako.

Bayan aika-aikatar da Najib ya aiwatar a gidan sai ya fito ƙofar gidan su riqe da taɓarya yana cewa duk wanda ya matso kusa da shi sai ya kashe shi, ko da maƙotaka suka yo kansa sai ya ruga ba inda aka kama shi sai kusa da jami’an tsaro na gidan gwamnatin Jihar Katsina, inda suka taimaka aka cafke shi kuma suka damƙa shi ga ofishin ‘yan sanda na GRA dake cikin garin Katsina domin cigaba da bincike.

Jami’an tsaron sun tabbatar da cewa wannan shine dalilin da ya sa wasu kafafen yaɗa labarai a makon da ya gabata suka bayar da rahoton cewar wani matashi ya je gidan gwamnatin jihar Katsina riƙe da tavarya yana neman Gwamnan Jihar Aminu Bello Masari don ɗaukar fansar mahaifiyarsa da ‘yan ta’adda suka kashe.

Majiyar Manhaja ta tabbatar da cewa Najib ya na shan miyagun ƙwayoyi wanda jama’a ke ganin hakan ne ya tunzura shi zuwa ga wannan aika-aikatar.

Yanzu haka dai mahaifin nasa Alhaji Umar Shehu Balele na kwance a asibitin koyarwa na Hwamnatin Tarayya dake Katsina yana karvar magani, ita kuma marigayiyar tuni a ka yi jana’izarta kamar yadda addini ya tanadar.