Gwamnatin Zamfara za ta kammala dukkan ayyukan da ta soma kafin ƙarshen wa’adinta – Kwamishinan Ayyuka

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Kwamishinan ayyuka na Jihar Zamfara Hon. Rabiu Garba ya yi fatan cewa dukkan abubuwa da aka cimma a taron ƙasa na ayyuka da aka gudanar a Kano za a aiwatar da su yadda zai amfani jama’ar ƙasar nan.

Ya ce a ɓangaren gudanar da ayyuka Gwamnatin Jihar Zamfara tana gudanar da aikin gina filin jirgin sama da samar da hanyoyi da zai kai ga filin jirgin wanda nan gaba kaɗan za a kammala ya zama jirgi na iya tashi kai tsaye daga Zamfara zuwa ƙo’ina a faɗin duniya.

Ya yi nuni da cewa  duk da cewa akwai wasu ƙalubale na aikin saboda magana ce ta kuɗi an fara aikin ƙasar babu kuɗi ga matsalar tsaro amma duk da haka Gwamna Matawalle yana iya bakin ƙoƙari ya ga an kammala aikin.

Kwamishinan ma’aikatar ayyukan da sufuri  na Jihar Zamfara ya ce duk da matsaloli na nan da can na tsaro amma suna ƙoƙari sosai don ganin cewa an kammala duk ayyukan da aka fara, abinda suke so kafin ƙarshen wannan wa’adi na farko na gwamna su ga ba su bar wani kwantan ayyuki ba.

Ya ce kamar yadda taken taron yake na cigaban ayyuka, duk ayyukan da Gwamnatin Zamfara ta ɗauko duka an kammnala, waɗansu kuma za a kammala su kafin ƙarshen wannan shekarar.

Kwamishinan ayyukan ya ce duk da akwai matsalar tsaro da aka samu jefi-jefi wajen gudanar da ayyukan amma suna amfani da jami’an tsaro domin bai wa masu aikin kariya.

Hon. Garba ya ce, yanzu matsalolin tsaro sun yi sauƙi a Zamfara, mutane na iya zuwa gonakinsu bisa irin ƙoƙarin da Gwamna Matawalle yake na yin magana da sasanta manoma da makiyaya duk da rigimar ‘yan ta’adda kaɗai. Akwai ayyuka na da dama da aka gudanar a ƙasa a Zamfara da aka yi da suke amfanar da al’umma.