Sallah mai yawan baya

A kwana a tashi yau duniya ta yi bankwana da azumin watan Ramadan an tsunduma a watan Shawwal. Allah mu na aara gode ma ka kuma mu na ƙara neman agajinka domin mu gajiyayyu ne. 

Shawara ta gyara kayanka ita ce, jama’a mu riƙa kula da kyau yadda rayuwa ke jujjuyawa tare da canjawa daga wannan hali zuwa wani. Misali a gabanka ga mutum mai wadata amma ya koma matalauci. Ga mutum mai lafiya a gefe guda ga wani cen ba bu lafiya, duka waɗannan darussa ne kuma abin lura ga mai hankali.

Ya kai wanda ya ciwo bashi domin kaɗai ya yi hidima ta sallah kuma musamman batun da ba abinci ne ba da fatan mu riqa waiga na ƙasa da mu ta hakan ne za mu rage dogon buri na duniya. Da fatan mu dunga ɗaukar rayuwa da sauƙi ganin a addininusulumci ba bu tsanani a ciki. Wassalam.

Daga Mukhtar Ibrahim Saulawa. 07066434519, 08080140820.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *