‘SANADIN KENAN’ (4)

Daga FATIMA ƊANBORNO

A wannan dare Mus’ab ya gagara runtsewa. Sai kaiwa yake yana komowa cike da saƙe-saƙen me zai je ya dawo. A wane hali Sulaiman ya bar Salima? Da sauri ya girgiza kai, ya ɗauki makullin motarsa ya yi falo da sauri.

“Kai Mus’ab! Ina zaka je a cikin daren nan?”
Gaba ɗaya ƙafafunsa sun riƙe ya rasa me zai ce mata. Dole ya juyo yana murmushi,
“Umma na mance abu a cikin mota zanje in ɗauko.”

Umma ta saki ajiyar zuciya mai ƙarfi wanda ya tabbatar masa da samun natsuwarta. Sannan ta nemi wuri ta zauna anan falon, ba tare da ta koma ciki ba. Dole ya tafi ya buɗe motar ya ɗauko takardun bogi da dama can a cikin motar ya bar su, sannan ya sake dawowa. Tana nan zaune ya yi mata sallama ya wuce ɗakinsa. Shi kansa yasan ba zai iya barcin ba. A hankali ya jawo wayarsa ya tura saqo kamar haka: “Ka ji tsoron Allah.”

Ya kife wayar kawai a ƙirjinsa yana jin bakinsa yana masa ɗaci. Kiran waya ya shigo, a lokacin da idanunsa suke a lumshe. Ko bai duba ba, ya san daga in da kiran ke fitowa. Kiran gaggawa a ke yi masa daga asibitinsu. Ba zai iya taɓuka komai ba. Dan haka ya ci gaba da rufe idanunsa.

Bayan Sulaiman ya gama kintsawa yana shirin zuwa ga Amarya, ya, ga saƙon text. Kamar zai share sai kuma ya tsinci kansa da son ganin saƙon menene, duk da zuciyarsa tana sanar da shi ba zai wuce na fatan alkhairi ba, kamar yadda a ka yi ta tururuwan turo masa saƙon taya murna akan aurensa.

Yana gama karantawa gabansa ya faɗi da ƙarfi. Gaba ɗaya ya mance da rayuwar wata Salima. Ya mance mata biyu gare shi ba guda ɗaya Asma’unsa ba. Kalamai ne marasa yawa, amma sun yi matuƙar tasiri a zuciyarsa. Tunawa da yadda suka yi kafin ɗaurin aurensa da Salima ya ƙara tsananta faɗar masa da gaba.

Tabbas ta sanar da shi bata da lafiya. A gigice ya juya da nufin fita. Asma’u ta dube shi sosai, domin ita angonta take jira don me ya sa zai fasa isowa gareta?
“Ina zaka je kuma?”
“Ina zuwa na yi mantuwan wani abu ne.”

Ya mayar mata da amsa tare da juyawa ya fice.

Da shigowansa in da take ya sameta bata motsi. Bai damu da warin da ke fita daga ɗakin ba, ya dinga girgizata. A gigice ya fito ya sami amaryarsa ya gaya mata abin da ke faruwa. Ta yamutsa fuska, “Dan makirci sai a daren farkona zata yi irin hakan. Ai wannan wulakanci ne.”

Ya kalleta cike da kwaɗayi da zumuɗi.
“Ki yi haƙuri bari mu kaita asibiti. Idan ta mutu Alhajinmu zai iya kasheni.” Dole ta ɗauko mayafinta, shi kuma ya ɗauki Salima da bata ko motsi, ya sakata a bayan mota. A yadda Asma’u ta ganta sai da gabanta ya faɗi, ta ƙara matsowa ta dubeta sosai ta ce,” An ya bata mutu ba? Dubi fa ka gani. Na shiga uku, Wallahi ta mutu.”

Sulaiman ya sake gigicewa. A take zuciyarsa ta karye. Abubuwan da ya dinga aikata mata suka dawo masa kai, ko da wasa bata tava gayawa kowa ba, bata tava nuna masa ta gaji da wulakancinsa ba. Tana yi masa biyayya iya gwargwado. Hawaye masu zafi suka zubo masa. Mahaifinsa mutum ne da yake da tsananin zafi. Duk duniya yana jin babu wanda hatta muryarsa ke firgita shi kamar mahaifinsa.

“Asma’u idan har Salima ta rasu na shiga uku. Mus’ab kaɗai sai ya kusa hallakani bare a kai ga mahaifina. Ina zamu kai haƙƙinta ni da Hajiyata? Mun cutar da ita, mun cutar da ita.”

Shi kansa wasu maganganun bai san yana faɗin su ba. Har suka iso asibitin su Mus’ab. Shi kansa gigicewa ya kawo shi asibitin, da yana hayyacinsa da ya guji asibitin Mus’ab ko domin gudun masifarsa.