Ya dace MƊD ta zamo dandalin warware matsalolin duniya

Daga SAMINU HASSAN

Yayin da aka ƙaddamar da cikakken zama karo na 77, na babban taron MƊD a farkon makon nan, kuma a karon farko da taron ke gudanar ido da ido tsakanin mahalartansa tun bayan ɓarkewar cutar COVID-19, masharhanta da dama na ganin lokaci ya yi da zauren MƊDr zai kara maida hankali, ga muhimman kalubaloli dake addabar duniya.

Tuni dai shi kansa babban magatakardar MƊD António Guterres ya amince da cewa, duniya na fuskantar mawuyacin hali, sakamakon ƙalubaloli iri iri da ake fama da su, musamman a fannin wanzar da zaman lafiya, da tsaron rayukan al’umma, da shawo kan annobar COVID-19 dake sake bazuwa, da kare haƙƙin bil adama, da shawo kan matsalolin sauyin yanayi, da samar da ci gaba mai ɗorewa ga kowa da dai sauransu.

Tun da dai shugabannin wannan babbar majalissa sun kwana da sanin halin matsi da duniya ke ciki, kuma su ne ke ɗauke da nauyin aiwatar da matakai na shawo kan waɗannan matsaloli, babu abun da ya dace illa su yi aiki tukuru, domin tabbatar da haɗin kan ƙasa da ƙasa, wajen cimma nasarar sauke alƙawura da majalissar ke ɗauka ga ɗaukacin bil adama.

Al’ummun duniya na fama da yanayi na yaɗuwar talauci, da rashin daidaito, da yunwa, da ƙalubaloli dake nuni ga buƙatar dukkanin sassa su haɗa kai da juna, domin “A gudu tare a tsira tare.

Kuma dandali irin na cikakken zaman MƊD, na ba da dama mai kyau ta tuntuɓar juna, da tunkarar matsalolin duniya tare.

A wannan karo ma, duniya na zuba ido ga MƊD, da fatan cewa, a matsayinta na zauren gudanar da haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa, majalissar za ta taka rawar gani wajen kyautata cuɗanyar sassan daban daban, har a kai ga cimma manyan nasarori, a fannin warware wasu daga manyan matsalolin dake ci wa duniya tuwo a kwarya.