Sauya sheƙa ba shi ne mafita ba, cewar Adamu ga sanatocin APC

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya roƙi sanatocin APC kan su yi haƙuri su daina ficewa daga jam’iyyar.

A ranar Larabar da ta gabata Adamu ya bi sanatocin har cikin Majsalisar Tarayya ya gana da su, bayan la’akari da yadda sanatocin APC suka ba da himma wajen sauya sheƙa zuwa jam’iyyun adawa, lamarin da ba zai haifar wa jam’iyyar ɗa mai ido ba.

Yayin ganawar tasu, Adamu ya roƙi sanatocin da ba su kai bantensu ba a zaɓen fidda gwanin jam’iyyar don shiga takara a babban zaɓen 2023, da su yi haƙuri.

Majiyarmu ta ce yayin taron, Adamu ya faɗa wa sanatocin cewa APC ta shirya wani shirin da zai shafe dukkan damuwar da faɗuwa zaɓen fidda gwanin ta haddasa musu, don haka babu buƙatar su fice daga jam’iyyar.

Idan dai za iya tunawa, batun zaɓen fidda gwanin da jam’iyyar ta gudanar cike yake da badaƙala, lamarin da ya yi sanadiyyar da daman sanatocin da ke da buƙatar komawa majalisa suka rasa wannan damar.

An ce sanatocin sun yi amfani da wannan dama wajen bayyana wa Adamu damuwarsu kan rashin dimokuraɗiyyar da ake fama da shi a jam’iyyar a matakan jihohi.

Adamu ya faɗa wa manema labarai cewa, ya yi matuƙar damuwa da yadda sanatocin suke ficewa daga jam’iyyar shi ya sa ya biyo su domin su tattauna matsalar.

Ya ce, sauye-sauyen jam’iyya abu ne da aka saba gani da zarar lokacin zaɓe ya ƙarato wanda hakan kan jefa shugabannin jam’iyya cikin wani hali.

Kafin zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar, sanatoci kimanin guda 70 ne APC ke da su a Majalisar Dartawa inda a yanzu suka rage 62, PDP na da 39, yayin da sabuwar Jam’iyyar NNPP ke da guda 3, YPP na da 2, sannan APGA da Jam’iyyar Labour kowacce na da ɗai-ɗai.