Sauya takardun Naira: Zainab ta ce babu ruwanta, ta gargaɗi CBN kan abin da ka iya biyowa baya

Daga BASHIR ISAH

Ministar Kuɗi, Kasafi da Tsare-tsare, Zainab Ahmad, ta nesanta kanta da matakin da Babban Bankin Ƙasa (CBN) ya shirya ɗauka na sauya tsarin wasu takardun Naira.

Haka nan, Ministar ta gargaɗi CBN da ya shirya tunkarar matsalolin da ka iya biyowa baya mudin ya aiwatar da sauya tsarin kuɗin.

Zainab ta yi waɗannan kalaman ne a lokacin da take yi wa Kwamitin Majalisar Dattawa kan sha’anin kuɗi jawabi kwanan nan a Abuja.

Yayin ganawarsu da Ministar, Sanata Opeyemi Bamidele mai wakiltar Ekiti ta Tsakakiya a Majalisar, ya ce kwanaki biyu kacal da bayyana ƙudirin sauya wasu takardun kuɗi da CBN ya yi, tuni Naira ta fara ɗanɗanar tasirin hakan ta hanyar faɗuwar daraja.

Ya ce darajar Dalar Amurka a kan Naira ta ɗaga daga N740 zuwa N788 kan Dala ɗaya sabosda tururuwar zuwa neman canji da ake yi.

Sanatan ya ce duk da dai ya gamsu da ƙudirin, sai dai a ganinsa ba a ɗauki matakin a lokacin da ya dace ba, musamman idan aka yi la’akari da halin da ƙasa ke ci a halin yanzu.

15 ga Disamban 2022, ita ce ranar da CBN ya ba da sanarwar zai saki sabbin takardun na Naira.

Takardun Naira da sauyin zai shafa sun haɗa fa N1000 da N500 da kuma N200.