2023: Za mu haɗa kai da INEC don daƙile sayen ƙuri’u – EFCC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa a Nijeriya (EFCC), ta ce za ta ci gaba da haɗa kai da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, domin daƙile ta’adar sayen ƙuri’u, musamman a lokacin babban zaɓen 2023.

Shugaban Hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa ne ya bayyana haka a wata hira da manema labarai a Abuja jiya Alhamis, jim kaɗan bayan kare kasafin kuɗin hukumar na 2023 a gaban kwamitin majalisar dattawa kan yaƙi da cin hanci da rashawa.

“Za mu ci gaba da yin abin da ya kamata mu yi, muna ƙoƙarin tabbatar da cewa  kuɗaɗen haramun ba sa samun damar shiga harkokin zaɓenmu,” inji shi.

Bawa ya ce hukumar za ta haɗa kai da INEC don kama wa tare da gurfanar da waɗanda ke da hannu wajen sayen ƙuri’u.

Shugaban hukumar ya ce ana ci gaba da shari’ar waɗanda aka kama da laifin sayen ƙuri’u a zaɓukan da suka gabata a gaban kotu.

Bawa ya kuma gode wa majalisar dokokin ƙasar bisa goyon bayan hukumar, ta hanyar wasu muhimman dokoki da aka tsara domin ƙara taimaka mata wajen gudanar da ayyukanta.