Daga SANI AHMAD GIWA Abuja
Bankin Duniya ya ce har yanzu talauci na ci gaba da ƙaruwa a Nijeriya duk da sauye-sauyen tattalin arziƙi da Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ta aiwatar domin daidaita tattalin arziƙin ƙasar.
A wajen ƙaddamar da rahoton ci gaban da aka samu a Abuja, Daraktan Bankin Duniya a Nijeriya, Mathew ɓerghis, ya bayyana cewa aƙalla mutum miliyan 139 ne ke rayuwa cikin ƙangin talauci a shekarar 2025.
Ya ce duk da cewa tattalin arziƙin Nijeriya ya ɗan bunƙasa, kuma gwamnati tana samun ƙarin kuɗaɗen shiga, yawancin jama’a har yanzu na fama da tsadar rayuwa da wahalhalu.
“Duk da waɗannan nasarorin, yawancin ‘yan Nijeriya har yanzu suna cikin wahala. ƙalubalen da ake fuskanta a yanzu shi ne yadda za a sauya waɗannan nasarorin zuwa inganta rayuwar kowa,” inji ɓerghis.
A gefe guda, bankin ya yaba wa Nijeriya bisa ƙoƙarin da ta yi wajen daidaita farashin musayar kuɗaɗen waje da rage giɓin kasafin kuɗi.
Sai dai ya ce waɗannan nasarori ba su kawo sauƙi ga rayuwar jama’a ba.
Ya shawarci gwamnati ta rage hauhawar farashin kayan abinci, ta yi amfani da kuɗaɗen jama’a yadda ya kamata, kuma ta faɗaɗa shirin tallafa wa marasa ƙarfi.
Rahoton, ya yi hasashen cewa tattalin arziƙin Nijeriya zai iya bunƙasa zuwa 4.4 cikin ɗari nan da shekarar 2027, ta hanyar bunƙasar noma, da masana’antun da ba su da alaƙa da harkar man fetur.
Amma ya yi gargaɗin cewa hauhawar farashin kaya da abinci na iya kawo wa waɗannan nasarori naƙaso.
