Shaidar kammala sakandare ta yi kaɗan ga batun tsayawa takara – Gbajabiamila

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Majalisar Wakilai ta Ƙasa, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya bayyana cewa duba da zamani yau, mallakar shaidar kammala makarantar sakandare ko makamancin haka a matsayin mafi ƙarancin zurfin karatu bai wadatar ba ga duk wani mai sha’awar riƙe muƙamin gwamnati.

Don haka ya yi kira da a yi wa Sashe na 131 (d) na Kundin Tsarin Mulki na 1999 kwaskwarima domin ɗaga mafi ƙarancin shaidar kartun da ya zama wajibi a mallaka kafin tsayawa takarar neman muƙaman gwamnati.

A cewar Gbajabiamila, tanadin shaidar karatu mafi ƙarancin da kundin tsarin mulkin ke nunawa a yanzu abu ne da ya shafi zamunnan baya amma bai yi nuni da abin da ake da buƙata a yau ba.

Gbajabiamila ya yi wannan bayani ne sa’ilin da yake gabatar da lakca a wajen taron bikin yaye ɗalibai karo na 52 na jami’ar jihar Legas (UNILAG) a ranar Litinin.

Ya ce, “Akwai buƙatar Majalisar Tarayya ta waiwai Sashe na 131 (d) na Kundin Tsarin Mulki na 1999 da zummar ɗaga mafi ƙarancin shaidar zurfin kartu ga masu sha’awar takarar shugabancin ƙasa da kuma sauran muƙamai nan gaba ya zamana shaidar karatun ta ɗara ta sakandare saɓanin yadda lamarin yake a yanzu.

“Yin hakan zai zama wani mataki na bunƙasa fannin zaɓe da inganta sha’anin shugabanci a ƙasa. Mu mai da hankulan wajen lura da manyan baubuwan da za su ciyar da mu gaba da kuma kyautata gobenmu.”

A nata ɓangaren, Shugabar taron, Justice Amina Adamu Augie, ta ƙalubalanci Gbajabiamila kan ya tabbatar da cewa hangen da ya yi ya tabbata a zahiri don cigaban ƙasa da al’ummarta.