Shugaban riƙo na ƙasa na jam’iyyar APC kuma Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya sanar da sabuwar ranar da jami’yyarsu za ta gudanar da babban taronta.
Idan dai za a iya tunawa, a ‘yan kwanakin da suka gabata ne Buni ya gana da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, inda a yau ya bayyana 26 ga Fabrairun 2022 a matsayin ranar da aka tsayar don gudanar da babban taron APC.
Jaridar Elanza ta ce sanarwar tsayar da sabuwra ranar taron ta fito ne Darakta-Janar na yaɗa labarai ga Gwamnan, Mamman Mohammed.