Shin wai me ke haddasa yunwa ne a nahiyar Afirka?

Spread the love

Assalam alaikum, ina roƙon Allah da ya ƙara ɗaukaka wannan jarida ta Blueprint. 

A gani na, cikin ‘yan shekarun da suka gabata, an sami raguwar mutanen da ke fama da ƙarancin abinci a nahiyar Afirka. Sai dai, matsalar ta sake kunno kai, inda a yanzu aƙalla mutane miliyan 26 ne suke fuskantar yunwa a nahiyar.

Wannan dai wata matsala ce da galibin akan iya fahimtar ta ne kawai bayan ta kau. Ga misali a ƙasar Kenya, an sami wani likita da wani malamin jinya da suka yi ƙoƙarin ceto wata yarinya wacce iyayenta suka shiga hali na damuwa saboda tsananin da ta fuskanta, inda ta kai bayan wasu ‘yan mintoci, ƙwararrun suka saduda tare da janye duk wani taimakon da suke yi wa yarinyar saboda tsanani. A ƙarshe dai sai kuka ne iyayen wannan yarinyar suka kama saboda rasa ta aka yi.

Shin mutane ne a matsayin sular yunwar? Rahotannin da suka yi nazarin lamarin, sun yi ittifaƙin cewa mutane ne suka haddasa matsalar ba kuma aukuwa ta yi haka nan ba. Wasu batutuwan kuwa sun haɗa da sauyin yanayi da ya shafi duniya da yawan sare itatuwa da dogaro da noman kayan abinci iri guda da ke zama wata matsala ga ƙananan manoma musamman.

Sai dai rigingimun siyasa sun fi yin mummunar illa galibi. ƙasashen Afirkar kuma da akasari ke cikin wannan rukunin, misali, Nijeriya da Sudan ta Kudu da Somaliya, su ne waɗanda ke fama da walau yaƙi ko kuma ƙoƙarin murƙushe matsalar ta’addanci. Cikin ƙasashen, gwamnatoci sun gaza bayar da hankalin da ya kamata a fannonin lafiya da ilimi da kuma tsaro. Maimakon hakan, ‘yan boko waɗanda ke hawa madafun iko na karkata dukiyoyi ne zuwa wasu ƙasashen masu ƙarfin arziki, don amfanin kansu.

Ni a gani, ya kamata Gwamnatin tarayyar Nijeriya da na Jihohin su ta shi haiƙan wajen ganin an daƙile matsalar ƙarancin abinci da ke ƙara kunne kai a ƙasar nan.

Daga MALAM AHMAD MUSA. 07041094323.

By ukarofi