Shugabar Tanzania za ta zama shugabar Afirka ta farko da za ta ziyarci Sin bayan babban taron wakilan JKS karo na 20

Daga CMG HAUSA

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Mao Ning ta bayyana a gun taron manema labaru a yau cewa, shugabar kasar Tanzania Samia Suluhu Hassan za ta zama shugabar ƙasar Afirka ta farko da za ta ziyarci Sin bayan babban taron wakilan JKS karo na 20.

Bisa labarin da ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin ta bayar, bisa gayyatar da shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya yi mata, shugabar ƙasar Tanzania Samia Suluhu Hassan za ta ziyarci ƙasar Sin daga ranar 2 zuwa 4 ga watan Nuwanba.

Mao Ning ta bayyana cewa, a shekarar 2013, yayin da shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya ziyarci ƙasar Tanzania, ya gabatar da tunanin nuna sahihanci ga Afirka, da hadin gwiwa, da goyon baya, da sada zumunta, da kuma daidaita matsaloli tare, a halin yanzu wannan tunani ya kasance tunanin manufofin Sin na raya haɗin gwiwa da ƙasashe masu tasowa.

A shekarun baya bayan nan, Sin da Tanzania sun kara imani da juna kan harkokin siyasa, da samun nasarori kan haɗin gwiwarsu, da kuma mu’amala kan harkokin ƙasa da ƙasa da yankuna.

Mai fassara: Zainab