Xi ya jagoranci shugabannin JKS zuwa tsohuwar hedkwatar jam’iyyar

Daga CMG HAUSA

Sakatare janar na kwamitin tsakiya na Jam’iyyar Kwaminis ta ƙasar Sin Xi Jinping, ya jagoranci mambobin zaunannen kwamitin ofishin kula da harkokin siyasa na kwamitin tsakiyar jam’iyyar, domin ziyartar Yan’an, wato tsohuwar hedkwatar JKS, wadda ke lardin Shaanxi na Arewa maso Yammacin ƙasar.

Xi Jinping, wanda kuma shi ne shugaban ƙasar, kuma shugaban rundunar sojinta, ya samu rakiyar wasu daga cikin shugabannin jam’iyyar da suka haɗa da Li Qiang da Zhao Leji da Wang Huning da Cai Qi da Ding Xuexiang da kuma Li Xi.

Sun kuma ziyarci wajen da babban taron wakilan JKS karo na 7 ya gudana, da gidan tsohon shugaban ƙasar Mao Zedong, da kuma ɗakin nune-nunen tunawa da juyin juya halin jam’iyyar na Yan’an, wanda ke ɗauke da tarihin lokacin da hedkwatar kwamitin tsakiyar JKS ke zaune a Yan’an, tsawon shekaru 13.

Mai fassara: Fa’iza Mustapha