An rufe kantin Jabi Lake saboda barazanar tsaro

Daga BASHIR ISAH

Rohotanni daga birnin tarayya Abuja, na nuni da cewa, barazanar tsaro ta sa an rufe katafaren kantin zamanin nan na Jabi Lake.

Hukumar gudanarwar kantin ce ta ba da sanarwar rufe shagon a shafinta na Instagram a ranar Alhamis.

A cikin sakon da ta wallafa din, hukumar ta ce an ɗauki matakin rufe kantin ne don kare rayukan ma’aikata da na kwastomomi.

Ta ce tana ci gaba da tuntuɓa da neman shawarwari daga hukumomin tsaron don samun daidaito kafin daga bisani ta sanar da lokacin da za a sake buɗe kantin.

Don haka hukumar ta ce tana amfani da wannan dama wajen bai wa abokan huldarta hakuri dangane da rufe kantin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *