Siyasar Bana a Nijeriya: Me ya kamata mu yi?

Daga NAFI’U SALISU

Shakka babu lokaci ya yi da ya kamata al’ummar ƙasata Nijeriya mu dawo cikin hayyacinmu. Dole mu yi karatun ta-nutsu domin ƙwatar ‘yancinmu a siyasance, da hikimance, hakazalika a ilmance. Sanin kanmu ne cewa, Nijeriya ƙasa ɗaya ce, al’umma ɗaya, sannan ƙasarmu ta kasance babbar ƙasa da ke ƙunshe da arziki, wanda da shi ne wasu ‘yan tsirarun mutane suke abinda suka ga dama.

Zuwa yanzu Nijeriya tana da shekaru 62 da samun ‘yancin kai daga Turawan Burtaniya (wato Turawan Mulkin-mallaka), waɗanda zuwansu Nijeriya ya yi matuƙar basu mamaki. Domin sun same mu cikin suttura da addininmu mai tsafta (Musulunci), sana’o’i da al’adu.

Duk da ana ganin cewa sun fara zuwa yankin Kudu na wannan ƙasa, amma kuma yankin Arewacin da suka zo daga baya sun yi abubuwa da dama waɗanda ba za a iya mantawa da su ba. A nan Kano muna da (British Council) sai Gidan Ɗan Hausa da kuma (Rumfa College) da sauransu.

Baya ga haka, mun ga irin gwagwarmayar da su Marigayi Sir Ahmadu Bello (Sardaunan Sokoto, da Tafawa Ɓalewa) suka yi domin ciyar da ƙasar nan gaba, musamman ma yankin Arewa. To sai dai kuma su shugabannin yanzu ba zamu iya cewa ga inda suka sa gaba ba, domin dai har yanzu abu ɗaya ne ake yin kamfen da shi wajen siyasa.

Shin mun rasa mutane masu kishi ne irin na su Sardauna, ko kuwa dai son kai ne da zalunci gami da rashin kishin ƙasa ya sa jagororinmu na yanzu ba ba sa damuwa da al’ummar ƙasa suke yin ta kansu kawai? Ko kuwa dai karin maganar nan ce da ake cewa; ‘RIJIYA TA BA DA RUWA GUGA TA HANA?’

Babban abin da ya fi damun mutane a yanzu, musamman a yankin Arewacin ƙasar nan, shi ne maganar rashin tsaro. Wannan shi ne babban tashin hankalin da yake samun kowanne ɗan Arewa, al’amarin da ya gagari kundila, kuma ya zamo tarnaƙi mafi ɗaga hankali da cire nutsuwa a zukatan al’ummar Arewa.

A jihohin da al’amarin ta’addanci ya yi tsamari, babu wasu alƙaluma na ƙididdiga da za su iya rubuta adadin rayukan al’ummar da ba su ji ba su gani ba suka salwanta.

Kasancewar muna fatan samun kyakkyawar ƙasa mai cike da adalci, hakan ba zai samu ba har sai mun tashi tsaye mun san ciwon kanmu, mu nemi mafitar da ita ce za ta kai mu gaci. Amma muddin muka kasance masu kwaɗayin abin duniya, da rashin kishin ƙasa da yankinmu, to tabbas babu yanda za a yi mu samar da kyakkyawar gobe ga ‘ya’yanmu.

Idan har muna son mu ƙwaci ‘yancinmu a gurin mutanen da suke wasa da rayuwarmu, to lallai ya zama dole mu tantance tsakanin tsakanin aya da tsakuwa. Abin da nake nufi a nan shi ne, duk wani ɗan siyasar da ya fito neman wata kujera a dukkan yankunan ƙasar nan, to yana da kyau mu kalle shi da kyau, sannan mu gano dame-dame ya yi wa al’umma na ci gaba don gina rayuwarsu. Yana da kyau duk wanda zai shugabance ka a kowanne hali, to ya kasance ka aminta da shi, ka yarda da shi, kuma ka tabbatar cewa yana da kyakkyawan fata ga al’umma. Wannan shi ne kaɗai zai kawo ƙarshen mulkin danniya da ba-ba-kere da ake yi a wannan ƙasa.

Shekaru da dama ‘yan siyasa suna neman haɗin kanmu da abubuwan da za su gina ƙasa, amma har yanzu abu ya faskara. Batu nake yi a kan (tsaro, ilimi, kiwon lafiya, kasuwanci, sufuri, wutar lantarki, ruwan famfo, hanyoyi da sauransu).

Duk wani ɗan siyasa sabo da tsoho idan yana kamfen da waɗannan abubuwan yake fakewa don a yarda da shi ya hau kujerar mulki. Talakawa da yawa ‘yan ƙasa ba su san yadda ake sarrafa kuɗaɗen ƙasarsu ba, dalili kuwa shi ne, saboda an bar su da tunanin yadda za suyi su rayu.

Duk wani ɗan Nijeriya talaka, kullum fafutukar da yake yi ba ta wuce ya ya zai samu abin da zai ci baya don ya rayu. Mutumin da aka dasa masa talauci, a ka bar shi da yunwa ta ya ya zai iya yin tunani a kan dukiyar ƙasarsa?

Tsadar rayuwa ta canza mutane, maimakon kullum al’umma su riqa kasancewa masu gaskiya da riƙon amana, sai suke zamowa marasa gaskiya da rashin amana, ba don komai ba sai don rashin adalcin shuwagabanninsu, domin an ce (DAGA NA GABA AKE GANIN ZURFIN RUWA).

Adalci shi ne farkon abinda shugaba zai yi a cikin al’ummar da yake mulka ya zauna lafiya, haka su ma al’ummar da yake shugabanta su zauna lafiya. Domin idan aka yi wa kowa adalci, to adalcin shi zai ci gaba da tafiya a cikin gidajenmu, kasuwanninmu da sauran wurare daban-daban da muke gudanar da rayuwarmu.

Amma rashin tsayar da adalci shi ne yake sa wa ka ga shugabanni ba sa iya yin yawo su kaɗai sai tare da masu gadi, ko a gida, ko a hanya, ko a wajen taro, da ko’ina a Duniya. Na tabbatar da cewa, da a ce shugabanni za su tsayar da adalci, to hatta a tsakanin talakawa sai gaskiya ta dawo, sai jinƙai da tausayi ya dawo, sai amana ta dawo.

Idan muka waiwaya baya, zamu ga cewa a shekarar 1993, ba sai mun koma baya da nisa ba, ƙasar nan babu inda za ka zaga ka zago face hankalinka kwance, ba ka da fargabar komai. Duk faɗin daji da duhunsa za ka iya kwanciya a cikinsa ba tare da wata fargaba ba.

Hakazalika yadda ake gudanar da al’amurran rayuwa. To amma yanzu fa, ga tarin dukiya a cikin ƙasa, ga tarin jami’an tsaro, ga tarin makarantun ilimi, ga asibitoci, ga kasuwanni a ko’ina, ga motocin hawa da jirage sama da na ƙasa, amma yin bacci a cikin salama ya gagari ɗan Nijeriya.

Don haka, matuƙar matasan ƙasar nan ba mu tashi tsaye mun sauya wa shuwagabanninmu alƙibla ba, to lallai nan gaba za mu kasance cikin fargabar da ba mu san yadda zamu ƙare ba. Don haka, mu yi amfani da lafiyarmu, da ƙwaƙwalwarmu, da hankalinmu wajen saita sahun ‘yan siyasa da masu riqe da madafun ikon ƙasar nan.

Ba kuma makami za mu ɗauka mu yi amfani da shi wajen sauya su ba, a’a! Magana ce ta cire kwaɗayin abin hannayensu a cikin zukatanmu, mu fuskance su gaba-da-gaba mu tabbatar da cewa sun samar mana adalci ta hanyar yin gaskiya a cikin sha’anin shugabanci.

Duk ɗan siyasar da yake neman mulki a duba a gani me ya yi na ci gaban al’umma kafin a zaɓe shi, sannan idan ma ya yi wa al’umma abubuwan gina rayuwa, to ya cancanta duk da haka ko bai cancanta ba? Domin abu ne mai kyau a zauna tare da wanda yake neman shugabanci, wanda yake son jama’a su zaɓe shi ya zama shugabansu, a tattauna da shi a ji me zai yi wa al’umma don ci gabansu? Idan ya faɗa ya zamto zai cika, sannan alƙawari ne ya ɗauka. Idan bai cika ba, jama’ar da suka zaɓe shi su tsige shi.

Amma ta ya ya za mu samu abinda muke so matuƙar ‘yan siyasa suna amfani da mu wajen bangar siyasa, da raba mana makami da kayan maye don mu yi musu aiki, sannan su raba mana kuɗi kuma mu ce muna so su yi mana aiki? Hakan ba zai yiwu ba, matuƙar muna son su ayi mana aiki, to mu rabu da abin hannunsu, mu rabu da yi musu bangar siyasa.

Kawai mu kalli cancantar mutum ba jam’iyya ko abin hannunsa ba, idan ya cancanta, kuma yana da nagartar da ta kamata a zave shi, to shi kenan sai a zave shi don ya zamo jagoran al’umma. Idan ba shi da nagarta, to sai a rabu da shi a zaɓi wanda ya cancanta.

Nafiu Salisu
Marubuci/Manazarci.
Ya rubuto daga jihar Kano.
[email protected]
[email protected]
08038981211