Ganduje ya haramta a adaidaita-sahu a Kano

Daga WAKILINMU

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya haramta zirga-zirgar adaidaita-sahu a wasu manyan titunan Kano.

Hukumar Kula da Ababen Hawa ta Kano (KAROTA), wannan doka za ta fara aiki ne daga ranar Laraba, 30 ga Nuwamba.

Bayanin hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da ta fito ta hannun mai magana da yawun hukumar KAROTA, Nabilusi Na’isa, wanda aka raba wa manema labarai ranar Talata.

Titunan da aka haramta wa ’yan adaidaita-sahun bi sun haɗa da Babbar Hanyar Ahmadu Bello, hanyar Mundubawa zuwa Gazawa da kuma hanyar Tal’udu zuwa Gwarzo.

Gwamnatin jihar ta maye gurbin adaidaita-sahun da motoci bas-bas guda 100 da ƙananan motoci 50 wanda za su ci gaba da jigilar jama’a zuwa wurare daban-daban.

Sanarwar ta ce nan gaba, gwamnati za ta sanar da haramta wa adaidaita bin sauran hanyoyin da suka rage da zarar ta shigo da ƙarin motoci.