Kwamishina ta buƙaci a hukunta Aisha Buhari kan badaƙalar gana wa ɗalibi azaba

Daga BASHIR ISAH

Kwamishina a Hukumar Kula da Harkokin ’Yan Sanada (PSC), Najatu Mohammed, ta yi kira da a hukunta matar Shugaban Ƙasa, Aisha Buhari, kan badaƙalar kamawa da gana wa Aminu Mohammed azaba da jami’an tsaro suka yi.

Da kuma kama tsohuwar hadimar Aisha Buhari kan soshiyal midiya, Zainab Kazeem wadda ita ma aka lakaɗa mata duka kan zargin fallasa sirri.

Aminu Mohammed matashi ne kuma ɗalibi a Jami’ar Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Najatu ta faɗa wa jaridar Daily Nigerian cewa abin da Aisha ta yi ɗaukar doka ne a hannu, don haka ta buƙaci jami’an tsaro su kama ta su kuma hukunta ta.

Ta ce wannan hali da Aisha ta nuna, abu ne da ya kamata ‘yan Nijeriya su tir da shi.

Ta ce, “Ba ta da ’yancin yin haka. Hasali ma, kamata ya yi a hukunta ta kan aikata hakan.

“Ina ganin ya kamata ’yan Nijeriya su tashi su nuna adawa da hakan. Ba za mu yarda sa zalunci ba,” inji ta.