Ƙungiyar ɗalibai ta nemi afuwar Aisha Buhari kan kama Aminu Muhammad

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙungiyar ɗalibai ta Ƙasa (NANS) ta nemi afuwar uwargidan shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Aisha kan tsare wani ɗalibin jami’ar tarayya da ke Dutse Jigawa, Aminu Mohammed da jami’an ’yan sanda suka yi.

Idan za a iya tunawa cewa, Hukumar SSS ta ce ta kama Aminu kan wani rubutu da ta wallafa a shafinsa na sada zumunta na yanar gizo da ta yi zargin ɓata sunan uwargidan shugaban Nijeriya, Aisha Muhammadu Buhari.

A cewar rahotanni, Aminu Adamu Muhammed ya yi a watan Yunin 2022, inda ya wallafa a shafinsa na Tiwita cewa ‘Buhari ta ƙara nauyi sosai bayan da ta taka rawar gani wajen wawushe dukiyar ƙasa yayin da talakawa ke sha wahala a ƙarƙashin mulkin mijinta’.

Muhammed ya wallafa cewa, “su mama an ci kuɗin talkawa an ƙoshi.”

NANS a cikin wata sanarwa a ranar Talata ta hannun shugabanta, Usman Barambu, ta nemi afuwar a madadin ɗaliban Nijeriya ga uwargidan shugaban ƙasar, yayin da ya kuma yi kira da a saki Mohammed.