Siyasar Kwankwasiyya: Bayan tiya akwai wata cacar

Daga RAHMA ABDULMAJID

A ranar da na yi sharhi a kan Atiku da Tinubu ‘yan kwankwasiya masu zuciya a hannu sun far min har da saƙonni cewa ban sanya madugu a sharhi na ba. Abinda na saba yi shi na yi, wato ƙyaƙyata dariya. Saboda ganin rashin adalci ƙarara da rashin tuna baya.

A 2019 na kasa haƙuri wajen nuna goyon bayan Kwankwaso ne ba don mutanensa ko shi ba sai don na yi na’am da ƙudirorinsa har ana min Laƙabi da ‘yar kwankwasiya. Kuma har yau da ni za a bai wa zaɓin Shugaban Nijeriya, Kwankwaso zan baiwa babu hamayya. Saboda, ƙwarewa, kuzari, da aiki musamman na gina ilmi da matasa. Sai dai kamar yadda kuka ce, Allah ne mai bayar da mulki, lallai Allah na iya ba shi, Yana kuma iya hana shi.

Idan muka koma kan zahiri kuma fa?

Da yake abin na matasa ne, bari mu fara daga Nazare. 

Na farko, a kundin tsarin mulkin Nijeriya ƙa’idar lashe zaɓen shugaban ƙasa ita ce lashe aƙalla kashi 25 na zaɓe daga kashi biyu cikin uku na jihohin tarayayyar Nijeriya. Wato ma’ana, Jihohi ashirin da huɗu. 

Na biyu, a lissafin tunggun siyasar Najeriya babi na ɗaya wanda ba a faɗi a Kwansitushan ba  shi ne, yankin da ɗan takara ya fito su ke zuba zallar quri’a, yayin da yankin da ba daga can ɗan takara yake ba nan ake  dambarwar samo kashi 25 zuwa 60.

Na uku, a wani shafi na lissafin tuggun siyasar ana samo waɗancan ƙuri’un  na kashi 25 ne ko ma fiye ta hanyar amfani da ƙarfin ‘ya’yan jam’iyya masu madafun iko a kowace jiha; kama  daga Kansila, ‘Yan majalisu, kwamishinoni  har zuwa gwamna Sannan Sarakunan Gargajiya da Malamai da wasu jagororin al’umma sai kuma tarin kuɗi da kan yi taron dangi wa neman wannan ƙuri’un .

Na huɗu, wani shafin tuggun ya nuna yadda iyalan yan takara kan zamo silar samun ƙuri’unsu. Misali, matansu da kan shiga lungu da sako wajen aminan zumunci da biki su samo musu ƙuri’ar nan mai shige da ‘1 to tell 10’ , wani lokacin ma zamantowar matan wasu ƙabilu ne da bana dan takara ba ko wasu addinai yana da tasiri. Misali, Atiku me mata huɗu masu mabambanta yare kowacce za ta janyo ƙuri’ar qabilunta. Haka ma Tinubu mai mata Kirista, ko ba komai, za ta tsakuro masa ƙuri’un coci.

Na biyar, ƙwarewar ɗan takara wajen shiga Lungu da sako tare da yin amfani da wasu yarukan da ba nasa ba ko da kuwa Turanci ne yana sanyaya zukatan masu jefa ƙuri’a. Mun ga hakan a siyasar OBJ ta farko.

Na shida, zubar da kan ɗan takara a gaban manyan mutane, ba kawai zuwa gaishe su yana laguda zukatan mabiyan babban mutumin su ji an girmama nasu su ma su girmama ka da ƙuri’a. Na tava halartan wani taro inda na ga malamin da ya yi gayyata na zaune a kan keke da yake yana fama da ciwon kafa, amma shi ɗan takarar da aka gayyata ya na tsaye a  kansa babu ko rusunawa ba ma ta girmamawa ba ta duba lalurar mutumin. Nan na ji mabiya na ta Allah wadai da ɗan takara mai girman kai.

Kada na cika ku da surutu, Idan waɗancan turakun gaskiya ne suna da tasiri a wanne ‘yan Kwankwasiyya ke da maki 20 cikin ɗari? 

Amma fa akwai wata cacar…

Ita wannan cacar ita ake kira ƙuri’ar raba gardama, ko ta kacalcali. Ita wannan ƙuri’a tana fitowa ne daga wani can siyasar yanki da kan dage ya kafa wata jamiyya ya tara mata jama’ar da ko da ba za ta iya cin kujerar shugaban ƙasa da kanta ba, za ta iya taimakawa wa wani ya ci ta hanyar amfani da wasu dabaru kamar haka:

Ko dai lumewa cikin wata  jami’yyar da ke neman cikon ƙuri’un in ya so sai a yi gyaran fuska, aƙida da manufa su zo ɗaya na wucin gadi. Za mu ga milsalin  hakan ko kwatankwacinsa a majar APC a 2014.

Ko kuma ta tsaya a gefe guda ta kacaccalawa dan takarar yankin da ta fi ƙwari, ƙuri’a. Misalin hakan shi ne salon da Tinubu da Malam Shekarau suka yi amfani da shi a 2011, inda suka taimaki Jonathan ya kayar Buhari. Inda Malam Ya tsaya takarar Shugaban qasa a ANPP, Ribaɗu ya tsaya a ACN, suka lalata aƙalla ƙuri’a milyan 2 da ‘yan kai. Ita ma wannan siyasar kamar saura, tana da amfani da rashin amfaninta, amma amfaninta ya fi yawa. Su ne kamar haka:

1- Samun isasshen lokaci na gina siyasar cikin yanki da haɗe yankin guri guda Kamar yadda muka ga ACN ta yi a Kudu maso Yamma.

-Samar da shugaban siyasa guda ɗaya maimakon ɗaɗaiku masu mabambanta muradu da manufofi.

-Samar da manhaja da alƙibla ɗaya ga yankin a hannun ‘ya’yan yankin da suka san ciwon yankin nasu.

-Ƙwato wa yankin wasu maƙudan haƙƙoƙi waɗanda idan ba kana da alƙalumman ƙuri’a ba, ba za a baka ba. Waɗannan haƙƙoƙi sun haɗa da ababen more rayuwa, kuɗin gina siyasa, Ilmi da sana’o’i.

-Samar da ɗan takarar da Idan fa Ya fito ya yi o a gyaran murya, to fa ko yana fama da cutar maƙyarƙyata sai an ba shi. Domin ya gina masu ƙwato masa haƙƙin da ma shi kansa ta inda ko Gwamnati me ci ta san karya shi na nufin take bakin farantinta ne da na ƙasa bakiɗaya.

-Samar wa siyasar yankin wasu kujeru na din-din-din da ba a isa a hana ba, inda su kuma ba su isa su kasa yi wa wanda ya kai su aiki ba.

Tsakanin neman shugabancin ƙasa da kafa siyasar yanki wanne Kwankwaso yake yi?

Duk da ban san Kwankwaso ba, ban san manufarsa ba, Amma ina fatan wannan siyasar ta yanki da raba gardama ce a ransa. Domin a nawa gurgun hangen, ina ga da shi da Jamiyyar NNPP da ma Arewa maso gabas sun fi buƙatar wannan siyasar fiye da takarar da babu tabbacin zai ci.

Amma Idan dai har siyasar yanki yake shirin kafawa, to fa da wahala ya dawo daga wannan yaƙi da kuturun bawa. duk da ya cika jamiyyar tasa da dangi da ‘yan ciranin siyasar da basu iya zama wuri ɗaya.

Sannan ina so a sani cewa, tururuwar da ‘yan Kwankwasiyya za su yi su yi ta jefa quri’a ga ‘yan takarar Madugu da Madugu  kansa ba zai zama asarar ƙuri’a ba, idan ba su zo da kofin wasan gida ba, za su ci tagulla a jihohin Arewa maso yamma, sannan za su ƙarfafa siyasar yankin kamar yadda Yarbawa suka yi. Domin haƙiƙa, ɗan takararsu mai jar hula tambarin ne wanda ko da jamiyya, ko babu sunansa Jamiyya ce maras gafaka.

Rahma Abdulmajid marubuciya/ mai sharhi a kan al’amuran yau da kullum. Ta rubuto daga Abuja.