Tinubu: Tsakanin takara da Musulunci

Daga FATUHU MUSTAFA

Baya ga batun rashin lafiyar ɗan takarar shugabancin Nijeriya na APC, Bola Ahmed Tinubu, yanzu kuma an kawo batun wai a matsayinsa na musulmi, bai taɓa gina masallaci ba, kuma ma wai ‘ya’yansa dukkansu kiristoci ne, saboda uwargidansa kirista ce.  A saboda haka, na ga akwai buƙatar mu warware zare da abawa a kan wannan batu da ya taso.

Na farko dai, ba ma batun auren bakitabiya a musulunci ba, wanda kowa ya san halal ne. Ba a Yarbawa ba ne kawai ake samu musulmi ya auri kirista har ma acikinmu yan Arewa. Misali, Alhaji Baba Danbappa har takaba ma ta yi masa. Alhaji Lema Jibril ma ya auri kirista.

Maigidan tsohuwar Ministan Kuɗi, Easther Nenadi Usman ma, sarkin yanka ne kuma musulmi. Dan haka ban ga inda auren kirista ya zama wani aibi ba. Kar kuma a manta, Jennifer Atiku matar Atiku Abubakar a yau tana Amurka tare da yayan da suka haifa, kuma ta koma addininta.

Abin tambayar a nan shi ne, meye makomar ‘ya’yan da suka haifa har uku? In ma har ‘ya’yan Asiwaju dukkansu kiristoci ne, ashe gidan kowa da akwai. Domin na yi imanin ba za a yi vari a kwashe dai-dai ba. 

Ba mu tava jin inda Asiwaju ya fito ya yi wata magana da ta soki addinin musulunci ba, amma kowa ya san musamman Atiku ya tara ‘yan jarida ya yi Allah wadai da batun shari’a da aka fara a Zamfara.

Ba a nan ta tsaya ba, ko kwanakin nan, mun ji yadda ya yi amai ya lashe a kan batun Deborah. Mun kuma tuna yadda ya fito ba kunya ba tsoron Allah ya ce a daina kiransa da Alhaji. A kawo mana wuri ɗaya da Tinubu ya taɓa irin wannan katoɓara. 

An ce Tinubu bai taɓa gina masallaci ba. Wannan zance akwai gyara a cikinsa. JIBWIS shaida ne, akan irin gudunmawar da ya basu a gidauniyar ginin masallacinsu a Abuja. Akwai ƙwararan shaidu da suka nuna ya bayar da gudunmawar gina masallatai da dama a ƙasashen Yarabawa.

Ya kamata a sani, gina mutum a wurin Allah ya fi gina masallaci. Kuma ba a buƙatar a gaya maka irin mutanen da Tinubu ya gina a ƙasar nan. Ko a kamfanoninsa na TVC da ‘The Nation’ kawai ya samar wa dubban mutane hanyar cin abinci. Baya ga a  fannin siyasa da ya kafa mutane da yau, suka zama sune masu faɗa a ji a siyasar Nijeriya.

Kama daga kan Mataimakin Shugaban ƙasa mai ci, zuwa ministoci da gwamnoni. Haka kuma duk da damar da ya samu ta ya bayar da sunayen mutane a ba su muƙamai, Tinubu bai tava tura sunan wani a danginsa ba, balle ma ya tura sunan ɗansa. Hakan na nuna cewa, abinda ke gaban Asiwaju shi ne, gina al’umma ba wai kawai gina kansa ba. 

Magana ta gaskiya, APC ta yi dacen dan takara da in har Nijeriya ta yi dacensa a matsayin shugaba, to ko shakka babu, za a samu sauƙin rayuwa da cigaba. Allah Ya bamu sa’a.

Fatihu Mustafa ya rubuto ne daga Abuja. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *