Ta hanyar biyayyar miji mace za ta samu duk abinda ta ke so – Halima Ben Umar

“Mata na fuskantar matsaloli yayin aiki tare da maza”

Daga AISHA ASAS

Yawaitar ƙalubale ga mata a yayin da suke aiki tare ko a ƙarƙashin maza ya jima yana kasancewa cikin al’ummar Hausa, wanda ya cancanci ya zama wutar da za ta cinye ilahirin burin mata na ɓangaren aiki. Da yawa daga cikin mata ƙalubalen na yin tasiri sosai a mafarkin zuciyarsu ta fuskar aiki, inda suke ajiye makaman yaƙi, su haƙura da burinsu. Duk da haka, akan samu jajirtattu daga cikin mata da suke iya jure wannan ƙalubale da ma wasu don tabbatar da ba su hana su isa ga gonar da za su girbe wahalar su ba. Hajiya Halima Ben Umar na ɗaya daga cikin mata da suka sha gwagwarmaya a rayuwar aiki tsakanin maza. Ƙwararriyar ‘yar jarida da ta riƙe muƙamai da dama. A wannan satin shafin Mata A Yau ya yi nasarar tattaunawa da ita, don jin rawar da ta taka, wadda muke fatan ta zama haske ga waɗanda ke fatan taka irinta. Mai karatu idan ka shirya, Aisha Asas ce tare da gimbiyarmu ta wannan mako kamar haka:

BLUEPRINT MANHAJA: Assalamu alaikum. Da farko dai za mu so ki fara da gabatar da kanki.
HALIMA: Wa alaiki salam warahmatullah. Sunana Halima Ben Umar. Kuma Ina da ƙungiya ‘Women in Media Cominication Initiatives’, wadda ni nake shugabanta.

Kasancewar wannan ne karo na farko da ki ka kasance tare da Blueprint Manhaja, za mu so ki ba mu tarihin rayuwarki.
To, alhamdulillah, ni dai an haife ni a unguwar Kankarofi, wato kusa da gidan Sarkin Kano. Na yi makarantar Gidan Makama Primary School. Daga nan na tafi Shekara Girls Primary School, wadda ta kasance ta kwana. Bayan kammala firamare, na wuce GGC Dala. Da na gama, kasancewar a lokacinmu ki na gama sakandare ake yi ma ki aure. Ni ma dai hakan ce, don Ina kammala wa aka yi min aure.

Bayan auren, da yake ni tun farko Ina da ra’ayin zama ‘yar jarida, sai dai maigidana ya ce, ba ya son aikin jarida, sai dai koyarwa. Sai dai ni gaskiya bana son aikin koyarwa, saboda Ina ganin ta a matsayin sana’a mai ɗan karen wahala, wadda ba kowa ne ke da ‘ilhamar’ koyarwa ba. Amma a lokacin da na sanar da mahaifina (Allah ya yi masa rahama) Ina kuka, sai ya ce, “duk wani abu da mace ta ke so daga mijinta zai iya yi mata ba tare da taimakon boka ko malam ba. Ta hanyar yi masa biyayya. Duk abinda yake so idan kika yi masa, za ki samu yadda kike so wurinsa.’

Da wannan na haƙuri, na zo aka kai ni makarantar fara share fage na koyarwa da ake yi a wancan lokaci. Na yi na gama. Sai kuma Allah ya kawo tafiya, muka bar ƙasa, zama ya mayar da mu Ƙasar Amurka. Inda muka shekara huɗu haka sannan muka dawo.

Da muka dawo ne na yi sha’awar koma wa karatu. Sai aka samo min ‘School of Technology’, inda na yi difloma a ɓangaren ‘Art and design’. Bayan kammala karatun, akwai wani Alhaji Mukhtar (Allah ya jiƙan rai) wanda shine MD ɗin NADA a lokacin. Shine ya tambaye ni, aka ce ai na ma kammala karatu. Ya ce in zo NADA in fara aiki.

A lokacin Ina da ciki sai nai ta kuka, don kamar yadda na faɗa a baya, ni aikin jarida ne burina, sai na ke ganin idan na je NADA na yi aiki kamar burin na wa ba zai cika ba. Har na roƙi maigidana kan ya ba shi haƙuri. Ya ce ba zai yiwu ya iya watsa masa ƙasa ga ido ba. Tunda har ya neme ni da kansa, to in yi haƙuri kawai in yi.

Cikin ikon Allah kuwa da na je sai aka tura ni ɓangaren su na ‘Cominication’, ya ce, tunda ‘Art and design’ na karanta, sai in dinga yi masu zane da kuma duba ‘News latter’ da ake yi.

Ko kin fuskanci wani ƙalubale a wannan aiki?
To kin san matsalar da mata suke fuskanta yayin aiki tsakanin maza, za ka ga ana nuna masu ƙyama ta ɓangaren yin aiki da su. Da abin ya yi yawa ne na gaya wa maigidana. Shine ya ce kawai in koma in yi digiri sai in bar aiki. Da wannan na koma Bayaru University’ na karanci ‘Mass Cominication’. Sai na dawo na ci gaba da aiki a nan dai NADA, sai dai na zama Ina ‘producing program’. In yi producing kuma in yi directing kuma in yi presenting duk ni kaɗai. Saboda duk ‘yan mazan da za su taimaka min aka hana su. Don haka komai ni ce. Idan na kammala duk aikin, in zo kuma in saka a rediyo, in saka a TV.

Akwai wani shiri da na yi na ‘Mu Koma Noma’ ni ce mace ta farko da ta fara irin wannan shirin. A lokacin mutane suka yi ta jinjina. Har lokacin kwamishina na yanzu shine shugaban NUJ, to mataimakin sa ya ce, lallai su je NADA, ayi masu godiya da jinjina don sun ji mace kuma ‘yar jarida, ta yi wannan shiri na noma, kuma na mata. To fa tunda aka yi wannan ba a sake bari na yi wannan shirin ba. Na talabijin ɗin ma daga baya aka zo aka rufe ni, na daina. A lokacin za ka ga idan za a fita aiki, za su dinga fita ɗai ɗaya, wai don kar a tafi da ni. Saboda kin san idan aka je wurin ciyaman na Local government ko wani akan samu ɗan alheri. To ni gaskiya bai damuna wannan, don na san da samu da rashi duk na Allah ne.

Akwai ma lokacin da na taɓa zuwa wurin marigayi Sheikh Aminudeen (Allah ya jiƙan sa) na tambaye shi kan halin da na ke ciki. Na ce aiki ne na ke yi, amma ba a ba ni aikin, kuma Ina karɓar albashi, to ko Ina cin haramun. Sai ya ce, ana ba ni aikin ne in ƙi yi? Na ce a’a. Ya ce in je in ci gaba da karɓar albashina halal ne na ke ci.

Ana cikin haka ne aka zaɓe ni a matsayin shugabar mata ‘yan jarida. Kuma kinsan cikin alfanun ƙungiyoyi na ‘yan jarida sukan samu tallafi daga wasu ƙungiyoyi na ƙasar waje. Kamar USAID, sai suka fara aiki da ƙungiyoyin mata ‘yan jaridu. Ana cikin haka sai suka zo suna neman ma’aikaciya a Kano, kuma suka nemi ni. Da farko na so in qi amincewa, amma maigidana ne ya ƙarfafa min gwiwa.

To ta yaya maigidan na ki ya canza ra’ayi, tunda a baya kin faɗa ba ya son ki yi aikin jarida?
Ai tunda na yi aiki a NADA yaga yanda muka yi. Kuma kamar yadda na faɗa a baya, biyayya ce nasarar kowacce mace. Kuma ni ita na riƙe, domin ko abu zan ba wa maigidana bana ba shi a tsaye, sai na duƙa. Duk wata tarairiya da kika sani don kyautata wa miji ba wadda bana masa. Sanadiyyar kyautata masa, shi kuma duk wani abu da na ke so zai mun. Duk wani abu da ya san zai sani farin ciki zai mun.

Hajiya Halima

To a tare da su na kwashe shekaru masu yawa, domin na fara tun a shekara ta 2000 har zuwa shekara ta 2017. A ɓangare ɗaya kuma muna ta aikin tamu ƙungiyar, wato Women in Media, inda na ke samo mana tallafi, muna ta ayyuka.

To, mu taɓo ɓangaren abinci. Wane abinci ki ka fi so?
Ɗanwake da mai da yaji, ba magi ba albasa, ba tumatar ba salad. Ɗanwake na asali, wanda za a sa wake, a sa dawa, a sa ƙwaruru, a haɗa shi da kanwa da kuka a niƙo.

Ɓangaren kayan sawa fa?
To, ni dai Ina son atamfa ko siket ko doguwar riga.

To Hajiya mun gode.
Ni ma na gode ƙwarai.