Ƙalubalen iyaye kan ’ya’ya mata masu shaye-shaye

ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Matsalar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi a tsakanin matasa ba baƙon abu ba ne, musamman ma ga ‘ya’ya maza, inda ya ke da mamaki da ɗaukar hankali shi ne a ga ’ya mace budurwa, bazawara ko matar aure tana bulayi cikin maye ko a ga tana ɗaga kwalba ana shewa da ita, babu ma dai kamar yarinya ’yar musulma kuma bahaushiya ko ’yar Arewa, da ake kyautata mata zaton ta taso a gidan tarbiyya, kunya da ƙyamatar irin waɗannan halaye marasa kyau.

Ba lallai ya zama abin kunya ga matan bariki ko masu zaman kansu da aka fi sani da karuwai ba, saboda dama su tuni sun fitsare ƙafafunsu, iyaye da sauran al’umma an sallama musu, saboda da salon rayuwar da suka ɗauka.

Sai dai abin takaici ne sosai, ka ga yarinya budurwa da ke zaune a gaban iyayen ta, kuma take samun kulawa da tarbiyya ta shiga irin wannan mummunar rayuwa, da sani ko ba da sanin iyayen ta ba, wato kenan tana ɓoyewa iyayenta da waɗanda suka san ta, don kada su fahimci ta sauka a layi.

Idan a baya ya kasance abin kunya da takaici to, a yanzu sai dai ya zama abin assha da ya kamata kowa ya ƙyamace shi. Ba lallai ne kowa ya yarda ba, amma ni na san ‘yan matan da yanzu suke shan wiwi da sauran sinadarai masu bugarwa da sa maye, fiye da maza, kuma kwakwalwarsu ta na ɗauka caraf, abin ya wuce yadda ake tsammani. Akwai wacce ma idan ta matsa sholisha a ɗankwalinta, sai a hankali.

Wani masanin lafiyar ƙwaƙwalwa Aliyu Alƙasim Yahuza ya bayyana cewa, akasari matasa suna suna shaye-shaye ne a saboda dalilai biyu, dalilin jin daɗi kamar yadda yanzu matasa ke yayin shan Shisha da wasu ke ganin ba komai ba ce ko kuma sigari inda wasu ke ɗaukar ta kamar ado, da dalilin da ya shafi ƙoƙarin kawar da wata damuwa ko neman cajin ƙwaƙwalwa, don yin wasu ayyuka na fasaha ko karatu.

Da yawan matasa, mata da maza sun ɗauki ɗabi’ar yi wa maganin tari da mura shan wuce lissafi ne saboda yadda suke son sauya rayuwarsu zuwa irinta wasu ‘yan gaba da fatiha da suke yi wa kallon sun waye, ko kuma su yi rayuwa irin ta abokai ko makusantansu ko domin kauce wa damuwa.

Kamar yadda wata matashiya ‘yar musulma a Jos ta tava gaya min cewa, tana fita ta sayi maganin tari da mura ba da sanin iyayen ta ba, don ta sha ta samu yin barci mai nauyi, saboda ta kaucewa yawan tunane-tunane da ta ke yi cikin dare a dalilin rashin samun aure da wuri.

Wata marubuciya daga Jihar Kano, Rahama Sabo Usman ta haɗu da wata ɗalibar Islamiyya mai ƙwazo da natsuwa wacce a dalilin rashin gata da rasuwar mahaifinta, ta fara tallan wainar gero inda a ta wannan hanyar ce ta gamu da wani saurayi mai halayyar shaye shaye wanda ya riqa nuna mata kulawa da soyayya har ya ja hankalinta kan yadda za ta fita daga damuwar da ta ke ciki, wannan shi ya jefa rayuwar wannan yarinya cikin muguwar rayuwar da ta yi sanadin mutuwar ta a wani mummunan yanayi.

Wata marubuciya Samira Bello Shinko a wani rubutu da ta yi game da illolin shaye-shaye ga al’umma ta bayyana wasu dalilai da ke sanya mutane shiga harkar shaye-shaye da suka haɗa da, shan magani ba da izinin likita ba, inda ta ce da yawa muna da wannan ɗabi’ar, da mun ji rashin lafiya sai muje Kemis mu sayo magani mu fara sha ba tare da likita ya gwada mu ya tabbatar mana da abin da za mu sha ko ya dace da jinin mu ba.

Rashin amfani da magani a kan ƙa’idar da aka dora mu shi ma wata hanya ce ta fara koyon shaye-shaye. Misali an ce ka yi sati ɗaya kana sha, sai ka yi kwana uku, ko kuma ka zarce adadin kwanakin da aka ƙayyade maka, ko kuma an ce ka sha cokali ɗaya sai kai kuma ka sha rabin kwalba.

Matsalar bai wa yara rashin kulawa daga ɓangaren iyaye, inda za ka ga wasu iyayen ba su damu da jan ’ya’yan su a jiki ba, har su san damuwarsu, irin wannan yana kawo matsalar da a Turanci ake kira ‘depression’, a bisa nazarin masana halayyar ɗan Adam.

Kuma hakan har wa yau ya zo daidai da fahimtar wata malamar makaranta Aishatu Suleiman Abubakar da ke Jos da marubuciya Rahama Sabo Usman da ke Kano, waɗanda ke ganin wata lalacewar tarbiyyar iyaye ne ke jawo wa, saboda rashin jan yaran su a jiki da ba su fuskar da za su a mayar da damuwarsu ko neman shawara.

Sannan kuma ana iya samun wannan matsalar a tsakanin ma’aurata da suke samun matsala ta fahimtar juna a tsakanin su, rashin samun waɗanda za su nemi shawara a wajen su ko yawan zurfin ciki, na daga cikin abin da zai sa wasu matan su fara shaye-shaye. Sakamakon yadda mijinta, kishiyarta, ‘ya’yan miji ko wasu abokan zama sun kuntuka mata sun tsangwami rayuwar ta, ta yi ƙoƙarin sanar wa iyaye ko makusantan ta halin da ta ke ciki an kasa fahimtar halin da take ciki.

Daga nan ne sai ka ga mata ta fara nemarwa kanta mafita tana shaye shaye, don ɗauke hankalinta daga damuwar da ke cin ta a rai. Wata kuma tana fara wa ne da shan magungunan ƙarin kuzari don ta samu zafin naman yin aikace-aikacen gida nata ko na mutanen da take yi wa aikatau, daga nan kuma in jiki ya saba sai a zarce da harka.

Mu’amala da ƙawaye ko abokan zama na cikin gida masu shaye-shaye a ɓoye shi ma yana janyo yawaitar wannan matsalar da bazuwar ta a cikin al’umma ba tare da an ankara ba. Wasu iyaye mata suna da sakacin shan magani barkatai idan suna da ciki, wanda hakan na iya raɓa jinjiri kafin ma ya zo duniyar an koyar da shi. Ko kuma mata masu ajiye magani barkatai a ko’ina suka ga dama, har yaro ya ɗauka ya fara sha ba tare da an lura ba.

Har wa yau, an gano cewa wani lokaci likitoci kansu suna janyo wanan matsalar ta hanyar haɗa mutum da maganin da jininsa ba zai iya ɗauka ba. A hankali kuma sai jikin mutum ya saba har ya ajiye kwalin maganin ko takardar likita ya riqa zuwa Kemis yana saye, ko da bayan ya samu lafiya.

Na haɗu da mutane da dama, waɗanda a zahiri idan ka gansu cikin karamci da sutura ta mutunci ba za ka tava yi musu tunanin suna suna shaye-shayen magunguna qara kuzari da ɗauke damuwa ba. Kamar yadda wata abokiyar aiki da na ke girmamawa daga Jihar Kano ta taɓa yi min tayin shan wasu ƙwayoyi masu saurin ɗauke gajiya da sa a ji garau, bayan wani aikin rangaɗi na zagayen duba wasu ayyukan wani ɗan siyasa. Saboda a ganin ta shaye-shayen ƙwayoyi ba ni abin damuwa ba ne, abu ne da ya zama gama gari, kuma ita ta saba, sai ta sha take barci.

Waxannan sune hanyoyi da wasun su da lokaci ba zai bar ni in faɗa ba, na daga cikin sanannun hanyoyin da ke hadddasa matsalar shaye-shaye a cikin al’umma. Kuma duk da ƙoƙarin da hukumar NDLEA mai yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ke yi, na faɗakarwa da kama masu kasuwancin wannan harka a birane da lunguna, abin kullum sai ƙara ta’azzara ya ke yi.

A wani bincike da tashar BBC ta gudanar a cikin shekarar 2019 a jihohin Kano, Legas, Jigawa da Kwara an gano yadda matasa, samari da ‘yan mata a Nijeriya suka mayar da shan kodin ya zama kamar leda, inda za ka gansu sun tsuma shi a robar lemon kwalba na Coca Cola ko Lacasera suna tafiya suna sha a titi babu wani babu tsoro ko fargabar wani abu.

Da yadda manyan kamfanonin haɗa magunguna ke haɗa baki da manyan dillalan irin waɗannan magunguna masu sa maye da bugar da hankali, ake kasuwancin su ta varauniyar hanya ba tare da sanin hukumomi ba.

Abdullahi Kwamanda wani mai aikin banga da taimakawa tsaro a cikin anguwanni da ke Jihar Filato Ya bayyana wa manema labarai irin yadda suka gano matan aure a cikin gidajen auren su ke cinikin kayan maye da tabar wiwi, ba tare da sanin mazajen su na aure ba.

Kamar yadda wani rahoto ya bayyana ƙoƙarin da wasu jami’an Hukumar Hisba ta Jihar Kano suka yi na gano wata mata da ke dillancin kayan shaye-shaye tana shiga gida gida inda take cinikin sa kamar wani goro.

Babu shakka wannan shaye shaye da ‘yan mata da matan aure ke yi yana kawo ƙaruwar mutuwar aure da ake kokawa a kai, da sanya yaran mata shiga harkar karuwanci da bin maza, yawan shiga rikici da mutane ko cin zarafin wasu ba tare da tunanin komai ba, saboda rayuwa cikin maye, taɓarɓarewar tarbiyar yara da faɗace-faɗace.

Ashe wannan zai nuna nana cewar matsalar shaye- shaye ba ƙaramar matsala ba ce ga rayuwar mu da zamantakewar iyalin mu, da al’umma baki ɗaya.

Wasu yaran mata, Zainab Bala ‘yar jarida da ke zaune a Babban Birnin Tarayya Abuja, da Aeeshat Abdulhamid Isma’il shugabar Gidauniyar Tallafawa Mata ta Sisters Support Foundation da ke Jos, sun koka da yadda wannan mummunar halayya ta shaye-shaye a tsakanin mata ke mayar da rayuwar mata baya da lalata musu tarbiyya, a matsayin su na iyayen al’umma.

Sun kuma bayyana buƙatar samar da cibiyoyin faɗakarwa da wayar da kai, da za a riƙa ƙoƙarin dawo da irin waɗannan matasa kan hanya madaidaiciya, domin gyara goben su, a matsayin su na ‘yan Adam da kuma lahirar su a matsayinsu na Musulmi. Yayin da marubuciya Rahama Sabo ke ganin akwai buqatar cibiyoyin ilimi suka qara mayar da hankali wajen buɗe ofisoshin ba da shawarwari ga ɗalibai na Guidance and Counseling, domin taimakawa matasa ɗalibai masu shaye shaye.

Malam Aliyu Alƙasim kuma ya sake qarfafa gwiwar gwamnati kan masu harkar sayar da kayan Shisha da a kafa musu wata doka da za ta tilasta su sanya wasu alamu ko hotuna da ke sanar da masu sha cewa rayuwar su na cikin haɗari, in suna cigaba da shan wannan abin, kamar yadda aka yi wa masu kamfanonin yin taba sigari. Sannan malamai da masu faɗakarwa a cigaba da ƙoƙarin wayar da kai don ganin an raba matasa da wannan mummunar rayuwa.

Wata ziyara da na kai Kano, tsautsayi ya shigar da ni wata cibiyar masu shan Shisha, na yi takaicin irin yadda na ga ƙananan yara ‘yan mata suna holewarsu, sun shagala wajen shaye-shayen da suke yi. Alhalin iyayen su na gida suna tunanin ko dai suna makaranta, ko wajen aika da gidajen ‘yan uwa, kamar yadda suka yi aaryar za su je.

Lallai ya zama wajibi iyaye su riqa sa ido sosai suna ganin abubuwan da ke faruwa da yaran su, musamman mata waɗanda gaba kaɗan su ne iyayen al’umma, dangane da yadda suke ruɗarsu da nuna halayyar kamun kai ko sanya sutura ta mutunci cikin hijabi da niƙabi, amma da zarar ka fita sai ka ci karo da su a Kemis ɗin mai sayar da Kodin ko wani sinadarin sa maye.

Idan yarinya ta ce miki za ta sayen magani ko kanta na ciwo, ki tabbatar kin ga irin maganin da take sha, kuma lokaci zuwa lokaci a riƙa bincika jakar ta ta makaranta ko ta zuwa unguwa ana ganin mai take fita ko shigowa gida da shi. Haka kuma idan sun shiga ɗaki da ƙawayen su an ji shiru, a riƙa leƙawa, don ta iya yiwuwa su mayar muku da gida dandalin shaye-shaye ba ku sani ba.