Ta ƙona kanta bisa zargin saurayinta da cin amana a Jigawa

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Wata mata ’yar shekara 35 mai suna Maryam Aminu ta conna wa kanta da kanta wuta bisa zargin saurayinta da cin amanarta a Dutse, Babban Birnin Jihar Jigawa.

Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar Sibil Difens (NSCDC) a jihar, Adamu Shehu, ne ya tabbatar da afkuwar lamarin ga manema labarai jiya Alhamis, 27 ga Afrilu, 2023.

Ya ce, lamarin ya faru da misalin ƙarfe biyu na dare a unguwar Gindin Ɗinya da ke yankin Ƙaramar Hukumar Dutse.

Ya ƙara da cewa, bisa binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa, matar ta kwarara wa kanta man fetur ne, sannan ta cinna kan nata wuta, yana mai ƙarawa da cewa, wasu maqota ne da suka kai agaji suka kashe wuta kuma tserar da ita.

“Duk da cewa, har yanzu ba a kammala tabbatar da sanin dalilin afkuwar gobarar ba, amma a na zargin cewa, lamarin yana da alaqa da saurayinta ɗan shekara 40 ne da ake kira da suna Ibrahim Haruna.

“Ta gamu da mummunar ƙonuwa mai mataki na biyu kuma a yanzu haka tana amsar magani a Babban Asibitin Dutse,” inji shi.

Wani wanda ya shaida lamarin da idanunsa mai suna Muhammad Yusif ya ce, matar ta yi matuƙar fusata ne a lokacin da ta ankara da cewa, saurayin nata ya je wajen wata macen daban.

“Karuwa ce mai azababben kishi a nan maƙotanmu. Ta yi zargin saurayin nata ya je ya ga wata macen ne. Don haka ta yi yunƙurin kashe kanta,” a cewarsa.

(NAN)