Yau wa’adin da Hukumar Alhazai ta bai wa maniyyata su kammala biyan kuɗaɗensu ke cika

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta bayar da wa’adin zuwa ranar Juma’a, 28 ga Afrilu, 2023, a matsayin ƙarshen wa’adin tura kuɗaɗen aikin hajjin shekarar 2023 daga maniyyata da kuma hukumomin kula da jin daɗin alhazai na jihohi.

Shugaban Hukumar NAHCON, Alhaji Zikrullah Kunle-Hassan, ne ya bayar da wannan umarni a ranar Larabar da ta gabata yayin gudanar da wani gagarumin taron tsere-tsare da shuwagabannin hukumar jin daɗin alhazai ta gudanar a gidan Hajji da ya ke Abuja.

A cewar wata sanarwa da mataimakiyar daraktar hulɗa da jama’a ta NAHCON, Fatima Sanda-Usara ta fitar, ta ce, taron an yi shi ne domin tattauna muhimman batutuwan da suka shafi kuɗaɗen da maniyyata ke aikawa n aikin Hajji domin kammala yawan waɗanda suka cancanci zuwa aikin hajjin 2023 daga Nijeriya.

Sanarwar ta yi nuni da cewa, tantance adadin zai nuna alƙaluman da za a qulla yarjejeniya da kamfanoninjiragen sama.

“A cewar Alhaji Zikrullah Kunle Hassan, hukumar za ta yi farin cikin yin aiki da duk wani adadin da za ta aika nan da ranar Juma’a, sannan ta rattaba hannu kan yarjejeniyoyin jigilar jirage zuwa Saudiyya a shekarar 2023 bisa ga wannan adadin.

“Ya bayyana cewa ana sa ran za a biya kashi 50 ga masu jigilar jiragen sama bayan sanya hannu kan yarjejeniyar yayin da wani kashi 35 zai biyo baya bayan tura jiragen da masu jigilar kaya suka yi.

“Babban jami’in hukumar ta NAHCON ya koka da cewa dole ne a yi la’akari da cewa duk wasu shirye-shirye sun dogara da adadin masu biyan kuɗin Hajji da aka tabbatar kafin kammalawa,” inji sanarwar.

Idan za a iya tunawa, an tsawaita wa’adin aika kuɗin Hajji a lokuta da dama tun daga watan Janairun 2023.