Takaicin yadda ake shugabantar al’umma ya sa na fito takara a PRP – Ali Rabiu Ali

Daga BABANGIDA S. GORA a Kano

Ɗaya daga cikin jikokin Marigayi Malam Aminu Kano kuma fitaccen jarumin wasan finafinan Hausa da ya daɗe ana damawa da shi a masana’antar, wato Ali Rabiu Ali ya bayyana cewa ganin irin yadda wasu shugabanni ke tafiyar da akalar shugabanci ya ɗauki hankalinsa wajen ba shi damar tsayawa takarar majalisar tarraya a mazaɓar Ƙaramar Hukumar Dala a Jihar Kano ƙarƙashin Jam’iyar PRP da Marigayi Malam Aminu Kano ya yi wa al’umma hidima a cikinta.

Daddy ya bayyana cewa lallai duk wanda ya san shi ya san ya fito ne daga tsatson gidan Malam Aminu Kano wanda yake matsayin kaka a garesa, wato mahaifi ga babarsa da ta haife shi, kuma da yawan mutane sukan danganta kansu da Marigayi Malam Aminu Kano don kyawawan halayensa nagari don mutum ya samu karɓuwa a siyasar shi.

Malam Ali ya kuma cigaba da cewa lallai yana ɗaya daga cikin muradan da suka sa ya fito takara a Jam’iyar PRP don ganin talaka irinsa ya samu wani dakalin da zai kai shi ga samun sauƙin rayuwa tare da hanyar da za a taimaka masa wajen cigaba da samun rayuwa mai inganci.

Fitaccen jarumin ya kuma ce a baya ba shi da ra’ayi na fitowa takarar wata kujera, mma tausayi da tausayawa ya ƙara ba shi damar tsayawa wannan kujera ta majalisar tarraya don tsamo al’ummar mazabarsa daga cikin irin riƙon sakainar kashin da da yawan ‘yan siyasa ke masu alƙawurra da dama lokacin yaƙin neman zaɓensu, wanda daga bisani da mutum ya yi nasara baka ƙara jin ɗuriyarsa sai idan ya dawo neman ƙuri’ar ku karo na biyu.

Ɗan takarar ya kuma bayyana ɗaya daga cikin ra’ayoyinsa na ƙirƙirar wani shiri na “Shugaba bawan talakka” ba don komai ba sai don ya fahimtar da jama’a cewa lallai duk wanda za su zaɓa to bawan su ne shi ya kamata ya yi masu hidima kuma ya gode masu ba su idan ya yi masu abuba su bishi da godiya kuma talaka ya kaishi wannan guri ne don ya kare masa muradinsa ba wai biyan buƙatarsa ba, a cewarsa.

“Ina fatan idan Allah Ya ba ni nasarar zama ɗan majalisar tarraya a Dala, Insha Allahu zan zama abin kwatance musamman wajen ara kare martabar kakana wato Marigayi Malam Aminu Kano da fuskar riƙe amana da kamanta gaskiya, kuma Ina roƙon Allah kada ya bani ikon danne haƙƙin al’umma lokacin da za a kyautata masu a wakilcin da suka turani.”

Daddy ya tabbatar da cewa lallai tunda aka dawo dimukuraɗiyya ba harkar gyara ake yi ba illa kawai su shugabannin suna yin abinsu ne don jari hujja, “amma gaskiya ba sa yi da jama’ar da suke mulka, kuma idan sun ce suna yi to Ina makomar wutar lantarki da ruwan sha a ƙasar nan tun wannan tsawon lokacin da har ya kawo yanzu ba a samu gyara ba?”

Ɗan jaridar wanda a halin yanzu yake neman goyon bayan jama’ar ƙaramar hukumar Dala ya nuna cewa batun da ake yi kuma saka farashin kuɗin takarar fom a jam’iyar dake ci a halin yanzu ya yi yawa, duk da cewa suma sauran jam’iyyun da ba haka suke saida nasu fom ɗin ba, amma kasancewar yanzu haka ba su da mabiya ya sa suka sassauta, ko kuma ya Allah suna buƙatar yi wa talakawa aiki ne ko sauƙaƙa masu tsayawa wannan takara a ƙarƙashin jam’iyyun.

“Kasancewar ɗan kasuwa mai jin tsoron Allah tare da tausayin talakawa ba zai iya ɗauko Naira miliyan ɗari ya sayi fom don tsayawa takarar Shugaban Ƙasa akan cacava ba, kuma har ma a ce sai an yi zaɓen fidda gwani idan ya yi nasara to shine yake da farkon tunanin kila yin nasara amma gaskiya abu ne mai wahala kasan sai dai a yi sha’ani kawai.”

Ali Rabiu ya kuma ƙara nusar da jama’a cewa lallai kowa ya sani duk wanda mutum zai zaɓa to ya sani akwai bayani da zai yi wa Ubangiji na dalilin da ya sa ya zaɓe sa tare da hujja kan wannan, don haka ya kamata kowa ya zaɓi wanda yake da inganci tare da tunanin sauya akalar jama’a zuwa ga hanya mai kyau.

Daga ƙarshe ya yi kuma kira ga al’umma musamman matasa da su farka daga baccin da suke yi na karɓar kuɗi don zaɓar wanda ba zai kai su ga ci ba, inda ya ce dole ne ya zama babu fa’ida ga masu sayar da ‘yancin su na rayuwa da kuma sayar da ‘yancin yaransu da sauran mutane baki ɗaya, wanda daga ƙarshe sai an yi da-na-sani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *