Tsakanin ECOWAS da Nijar: Abubuwa 7 da ya kamata mu sani

  1. Ba ‘yan Arewa ne kawai ba sa son yaƙi da Nijar ba, Yan kudancin Najeriya na adawa da shiga yaƙin kuma suna amfani da shafukan da suka fi tasiri irin Twitter, Tiktok da jaridu wajen bayyana haka. Sai dai damuwarsu ba ta taƙaita a zumuntar Nijeriya da Nijar ba, akasarin sun fi damuwa da ganin Rasha da Faransa ne za su yi amfani da ‘yan Afirka su yaƙi junansu a madadin muradunsu. Don haka, kada garin ƙoƙarin raya zumuncinmu da Nijar mu haifar da ƙabilanci a cikin gida.
  2. Ƙoƙarin korar wata ƙasar Turai da gayyato wata da ƙasashen yammacin Afirka suke yayin yi shi ma ba hanya ce mai vullewa ba, hasali ma kira wa kai ruwa ne. Su turawan suna da fahimta mai hankali da yin komai da tsari ta inda ko satar za su yi maka a ƙasa, idan ka ga ɗaya ta koka to ba a raba da maslaharta ba ne. Don haka, a natsu a bibiyi wannan lamari da hankali ba da tausayi zalla ba lokaci zai bayyana mana ko sabbin jinin na gayyato mana sabon mulkin mallaka ne ko kuma ‘yanci
  3. A Yanzu da Nijar ke ƙarƙashin Mulkin Soji babu isasshen ‘yancin Faɗin albarkacin baki da zai iya nuna mana cewa, shin duka ‘yan Nijar ke son Mulkin Soji ko kuwa akwai masu adawa da su? Tunda babu abinda Mulkin Soja baya jurewa irin adawa, wannan ya sanya hukuncin da ake yi da ganin zanga-zangar nuna goyon baya ba za ta zama dalili na cewa Nijar ɗin Mulkin Soji take so ba
  4. Ƙasar Nijar ba irin Burkina da Mali ba ce, tana da matuƙar muhimmanci ta fannoni da dama da zai yi wuya ƙasar da ta san ciki da falon Nijar sama da shekaru 100 kamar Faransa ta kuma ke da muradu a ƙasar ta ƙyale wata sabuwar ƙasa da ba ta san Afirka ba sai ta nesa ta zo ta ƙwace mata wannan ƙasa. Don haka, ina ga taka-tsan-tsan da Diplomasiya ya fi a bi daga a bar Nijar din ta sanya kanta a hanyar zama naman da kuraye biyu za su fafata a kai.
  5. Idan ba ku manta ba, tun bayan katsewar Iskar Gas daga Rasha sakamakon yaƙin Ukraine, kallo ya koma Afirka musamman Najeriya wadda za ta bai wa turawan Iskar Gas da zai riqa bi ta Nijar zuwa Maroco zuwa Turai. Idan Nijar ta yanke wa turawa wannan garavasar ana nufin idan sanyi bana ya zo su zama kankara kenan ba su Gas me ɗumama rayuwa? Kuma kuna ganin Turawan za su sanya ido hakan ta same musu? A bi a hankali Don Allah.
  6. Uranium ɗin Nijar na daga cikin kashi mai tsoka na makamashin da Faransa ke dogaro da shi wajen samar wa Kanta wutar lantarki na awoyi 24 ba tare da yankewa ba, amma kuma Ita Nijar din ta bar ta babu wuta sai Najeriya ta ba ta kashi 70 cikin 100. Ta yaya aka bar Faransa ke cin karenta babu babbaka haka na tsayin wannan shekarun? Lallai Ingila saliha ce ashe. Amma kuna ganin kawai haka aka bar Faransan ko ta tanadi wani abu ne da ake tsoro?
  7. Rasha fa ba za ta yi wani gagarumin abu don ceto ƙasashen da ke kira gareta ba a yanzu saboda dalilai da dama. Ciki kuwa har da kasancewar ita ma tana fuskantar yaqin taron dangi da duk da tana matuqar ƙoƙari, amma yana lamushe ƙarfinta, ta inda a wani abu mai kama da juyin Mulki har shi Shugaba Putin sai da ya fuskanci barazana a cikin gida. A irin wannan yanayin ƙasar Rasha ba za ta yi watsi da wasu ƙasashen Yammacin Afirka ba ta ɗauki wasu, Musamman ma a ce ta ɗauki mabuƙata ta bar masu gwaɓi-gwaɓi wa Amurka da ƙawayenta, wannan ya sanya duk da zarya da matasan sojojin ke yi zuwa Rasha, Rashar na nuna goyon baya ga ECOWAS da lallashinta da ta yi amfani da Diplomasiya, Su dai masu kiran za a ba su damar ganawa da shugaba Putin da kuma abinda ba a rasa ba.

Wadannan hasashen nawa babu abinda suke kira a kai da ya wuce a bi a hankali kada masu kira da a ƙyale Nijar su zamo silar jefa ta a uku gobe.
Allah Ya karya Azzalumai

Rahma Abdumajid, Marubuciya/manazarciya ce kuma mai sharhi a kan lamurran yau da kullum na siyasa da zamantakewar al’umma. Ta rubuto daga Birnin Tarayyar Abuja.