Wanda ya zana tutar Nijeriya, Pa Taiwo Akinkunmi ya kwanta dama

A wannan Laraba aka sanar da rasuwar Pa Akinkunmi wanda ya zana tutar Nijeriya mai ɗauke da launin fari da kore.

Marigayin ya bar duniya yana da shekara 87.

Ɗan marigayin mai suna Samuel Akinkunmi me ya sanar da rasuwar mahaifin masa a shafinsa na Facebook.

Pa Akinwumi ɗan asalin Owu ne a Abeokuta, Jihar Ogun, wanda aka haife shi a ranar 10 ga Mayun 1936.

A halin rayuwarsa, marigayin ya yi karatu a gida da kuma ƙetare.

A ranar samun ‘yancin kan ƙasa, wato 1 ga Oktoban 1960, aka ɗaga tutar Akinkunmi ya tsara a madadin ta turawan mulkin mallaka.

Gwamnati a wancan lokaci, ta yi wa Akinkunmi kyautar Pan 100 sakamakon cira tuta da aikinsa ya yi a tsakanin na takwarorinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *