Tseren gasar Firimiya ya koma hannun Man City

Daga MAHADI M. MUHAMMAD

Manchester City ta doke Arsenal 4-1 a wasan mako na 33 a gasar Firimiya ranar Laraba a Etihad.

Minti bakwai da take leda Kevin de Bruyne ya fara cin qwallo, sannan John Stone ya qara na biyu daf da za a je hutu.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Kevin de Bruyne ya ƙara na uku na biyu da ya ci a fafatawar.

De Bruyne ya ci Arsenal ƙwallo bakwai a Premier League jimilla, ƙungiyar da yafi ci ƙwallo a babbar gasar tamaula ta Ingila.

Arsenal ta zare ɗaya ta hannun Rob Holding, saura minti huɗu a tashi daga wasan, sai dai daf da za a tashi Erling Haaland ya ƙara na huɗu.

Ƙwallo na 33 da Haaland ya zura ƙwallo a raga a Premier League kawo yanzu.

Haaland ya zama kan gaba a cin ƙwallaye da yawa a kaka ɗaya a Premier League a tarihi.

Jerin waɗanda suka ci ƙwallaye da yawa a kaka ɗaya a Premier:

 • Ƙwallo 33 – Erling Haaland (2022-23)
 • Ƙwallo 32 – Mohamed Salah (2017-18)
 • Ƙwallo 31 – Luis Suarez (2013-14)
 • Ƙwallo 31 – Cristiano Ronaldo (2007-08)
 • Ƙwallo 31 – Alan Shearer (1995-96)

Wannan shine karo na uku da City ta yi nasara a kan Gunners a bana, inda ta fitar da Arsenal a FA Cup a cikin Janairu.

City ta doke Arsenal 3-1 a cikin watan Fabrairu a Emirates da kuma ranar Laraba da City ta ƙara cin Arsenal 3-1 amma a Etihad.

Da wannan sakamakon Arsenal ta ci gaba da zama ta ɗaya a teburin Premier League da maki 75 da tazarar maki biyu tsakaninta da City mai kwantan wasa biyu.

Wasa uku da City ta ci Arsenal a bana:

Firimiyar Laraba 26 ga watan Afirilun 2023

 • Man City 4 – 1 Arsenal
 • Premier League Laraba 15 ga wata Fabrairun
 • Arsenal 1 – 3 Man City
 • FA Cup Juma’a 27 ga watan Janairun 2023
 • Man City 1 – 0 Arsenal

Ranar Lahadi 30 ga watan Afirilu Fulham za ta karɓi baƙuncin Manchester City, ita kuwa Gunners za ta kece raini da Chelsea a Emirates ranar 2 ga watan Mayu.

Sauran sakamakon wasannin ranar Laraba a Premier:

 • Nottingham Forest 3 – 1 Brighton
 • Chelsea 0 – 2 Brentford
 • West Ham 1 – 2 Liverpool