Tunasarwa ga ‘yan Arewacin Nijeriya: Takenmu shi ne aiki da Ibada

Spread the love

Daga YUSUF MUHAMMAD DOSARA

Abinda tambarin Arewa (Arewa logo) yake nufi shi ne; haɗin kai daka ɓangarori mabanbanta.

Yankin Arewacin Najeriya yanki ne mai cin gashin kansa a cikin Najeriya, wanda ya sha bamban da yankin kudancin Najeriya. Arewacin Nijeriya na da al’adu masu zaman kansu, sannan suna hulɗa da ƙasashen waje da kuma tsarin tsaro mai kyau.

Yankin Arewacin Nijeriya nada kimanin girman da ya kai 660,000 km2 (250,000 sq mi).

Tun a shekaraun 1990s yankin Arewacin Nijeriya na da kimanin adadin mutanen da suka kai miliyan tara (9,000,000).

Manyan yarurrukan dake cikin Arewacin Najeriya dai sun hada; Fulani, Kanuri, Igala, Igbira, Nupe, Gwari, Hausa, Birom, Margi, Jukun, Katab, Babur da sauransu.

Duk da yake yanki Arewacin Nijeriya ya kasance yanki ne mai mabanbantan qabilu da addinai, kuma ya kasance yanki ne mai rinjaye na musulmi akwai kiristoci da dama suna a cikin wannan yankin. Hausawa, Fulani da Nupe sune kabilu ma fi rinjaye a wannan yankin na Arewacin Nijeriya.

Yankin Arewacin Nijeriya yanki ne mai ɗimbin tarihi mai ban sha’awa. Yanki da babu komai a cikin sai soyayya da kaunar juna, yanki da babu komai a cikin shi sai tausayi da kyautatawa juna, yankin da babu komai acikin shi sai zaman lafiya da riƙon amana.

Kafin zuwan wannan lokaci da Allah ya kawo mu, duk mutumin da yake yankin Arewacin Nijeriya bai san me ake cewa tashin hankali ba, babu abunda ya sani face zaman lafiya da kwanciyar hankali. Ɗan Arewa bai san ya ake faɗa da kashe-kashen juna ba, sai dai ya ji labarai a gidajen radio da talabijin.

Yankin Arewacin Nijeriya yanki ne wanda Allah ya albarkace shi da tarin arziki da kuma ƙabilu daban-daban, kuma dukansu suna zaune waje guda, cikin kwanciyar hankali da lumana. Hakazalika, akwai mabanbantan yaruka kuma kowa na ƙaunar juna.

Yankin Arewa yanki ne da Allah ya albarkace shi da matasa masu ilimi da neman na kansu, matasan masu hankali da natsuwa da saninn ya kamata, matasa masu kishin kansu da al’ummar yankinsu, matasa masu tashi tsaye komai wuya komai daɗi su nemi halak domin kare mutuncin kansu da na ‘yanuwansu, matasa masu kunya, tausayi da riƙon amana.

Matasan Arewa kowa na da sana’ar yi, wasu manoma ne, wasu makiyaya, wasu wanzamai, wasu maƙera, wasu mahauta, wasu masaƙa, wasu jima suke yi, wasu kuma rini, wasu ɗinkin kayan sawa, wasu kuma ɗinkin hula, wasu ‘yan kasuwa wasu kuma fatake ne.

Wannan dalilin ne ya sa kowa na ƙaunar wannan yankin, kowa na marmarin abunda zai sa ya zo ya zauna a wannan yanki na Arewacin Nijeriya, wannan dalilin ne ya sa wannan yanki na Arewacin Nijeriya ya yi ya cigaba a wancan ƙarnin da muka baro a baya.

Yau zan yi magana ne a kan wasu ƙabilu biyu, ko kuma ince yare guda biyu a yankin Arewacin Nijeriya, waɗanda bama ka iya banbanta su, ba ka iya ware al’ummar wannan wabilar da waccen ƙabilar, saboda zamansu tare a waje ɗaya kuma zama na amana, saboda babu amanar data kai ta auratayya.

To waɗannan ƙabilu guda biyu sun kasance kowanne na auren kowa, ka ga kuwa an zama ɗaya, ba wasu ƙabilu nake nufi ba, face Hausa da Fulani.

Saboda wannan kyakkyawar alaqar dake tsakaninsu ne ya sa sunan ƙabilun aka hace su waje guda aka mai da su ƙabila guda wato Hausa Fulani.

Wani abun ban sha’awa a tsakanin waɗannan ƙabilun guda biyu shi ne, hatta hanyar aikinsu don gudanar da rayuwar su ta yau da gobe duk kusan ɗaya ne, saboda su dai Hausawa sana’arsu ita ce noma, su kuma Fulani, kiwo.

To ka ga da manomi da makiyayi ai duk abu ɗaya ne, saboda sai manomi ya yi noma sannan dabbobi za su ci kara ko haki. Su kuma dabbobi sai sun yi kashi sannan za a samu takin da za a saka a gona domin samun amfani mai kyau.

Haka waɗannan ƙabilu suka yi rayuwa gwanin ban sha’awa na tsawon shekaru,
Amma yanzu wai waɗannan ƙabilun ne suke faɗa da junansu, waɗannan ƙabilun ne suke yakar junansu, waɗannan ƙabilun ne suke kashe junansu, subhanallahi!

yanzu Arewa ta zama gidan yan ta’adda Arewa ta zama yankin tashin hankali, Arewa ta zama yankin da ake tsoron shiga, Arewa ta zama yankin da babu wata sauran amana tsakanin ƙabila da wata ƙabila, yanzu an kai ga ɗan Arewa yana shakkun faɗan cewa, shi ɗan Arewa ne idan ya shiga wani yankin, wa’iyazubillahi.

A iya sani na, ana yaƙi ne ko kuma faɗa saboda wani abu misali saboda addini, ko kuma, ƙabilanci, ko kuma saboda wani yanki, ko kuma saboda wani dalili mai ƙarfi, amma banda yaƙi da kuma tashe-tahsen hankulan dake faruwa a yankin Arewacin Nijeriya.

Ya kamata mu tsaya mu lura mu duba lamarin nan, a duk tarihin yaƙe-yaƙe da aka yi da kuma waɗanda ake yi yanzu a Duniya, babu wani yaƙi da ake yi babu gaira babu dalili, sai yaƙin da aka kunna a tsakanin Hausawa da kuma Fulanin yankin Arewacin Nijeriya.

Kashe-kashe, Arewa, sace-sace, Arewa; garkuwa da mutane, Arewa; faɗan ƙabilanci, Arewa; fadan addini, Arewa; bangar siyasa, Arewa; rashin Ilimi, Arewa; rashin sana’a, Arewa; rashin aikin yi, Arewa; rashin tausayi, Arewa; shaye-shaye, Arewa; talauci, Arewa; yunwa, Arewa; barace-barace, Arewa; ga damfara yau duk a cikin yankin Arewacin Nijeriya!

Rikicin da ake yi, da kashe-kashe da sace-sace a yankin Arewa Wallahi tallahi hatta masu yin sa ba za su iya faɗa maka dalilin da ya sa suke yin wannan aika-aikar ba. Wallahi akwai harin da za a kai, a kashe mutane, shi kansa wanda ya yi kisan bai san dalilin da ya sa ya yi kisan ba balle kuma shi wanda aka kashe!

Ya kamata mu tsaya mu fahimta, kuma mu lura da cewa, duk fa wanda ya yi amfani da mu yau ya cutar da ‘yan uwanmu, to mu ma gobe zai iya yin amfani da wasu domin ya ga ya cutar da mu. Idan kuwa haka ne, ya kamata mu tsaya mu kare kanmu da ‘yanuwanmu mu zama masu kishin kanmu.

Duk da Wallahi kashi 80 cikin 100 laifin na shuwagabannin yankinmu na Arewa ne, saboda son kai da son zuciya ya yi musu yawa. Ba su da imani ba su da tausayi kuma ba sa jin tsoron haɗuwar su da Allah mahalicci, saboda inda suna jin tsoron haduwarsu da Allah to da ba za a rinqa kashe al’umma bayin Allah a yankunansu ba kuma a ƙarƙashin mulkinsu ba, amma su ja baki su yi shiru, saboda ba nasu aka tava ba.

Yanzu al’ummar yankin Arewacin Nijeriya har sun manta menene romon Dimokuraɗiyya, kai akwai ma waɗanda da yawa ba su san shi ba.

Akwai yaran da da yawa ba su san menene zaman lafiya ba, ba su san menene ilimi ba, basu san da cewa idan an mutu akwai hisabi ba, kuma basu san menene daɗin Duniya ba, suna cikin daji dauke da makamai, akwai wanda ma shi tunaninshi kawai abunda aka zo yi Duniyar kenan, a yi kashe-kashe a koma shikenan, saboda bai san lokacin da ana zaman lafiya ba, kuma bai je makaranta an karantar da shi ba, to ta yaya muke tunanin za a zauna lafiya acikin wannan halin?

Kun bar al’umma ba ilimi’ babu asibitoci ingantattu domin kiwon lafiyarsu, kun kasa samar da aikin yi ga matasa, ga rayuwa ta yi tsada, kuma kuce wai talaka ya zauna lafiya, ni a gani na abu ne mai wahala!

Ka bar mutum da yunwa sannan ka ce masa ya jira ka ka dawo sannan ya ci abinci, kuma shi kansa ya san ba dawowa za ka yi ba, idan fa yunwar nan ta fi ƙarfinsa, to dole ya yi duk yadda zai yi ya ci abinci, in ya so daga baya koma me zai faru, ya faru.

Wallahi tallahi kashi 60 cikin 100 na ‘yan ta’addan dake yankin Arewacin Nijeriya ba wai suna shiga harkar ta’addacin ba ne saboda son ransu ko kuma saboda jin daɗin duniya ko kuma don su tara dukiya,, a’a, suna shiga ne kawai saboda ba su da wani zaɓin da ya wuce wannan, saboda ko sun yi ta’addancin, ƙarshe dai kashe su za a yi. Idan kuma suka ƙi yi suka zauna a gida cikin karkara, yunwa ce za ta biyo su ta kashe su.

Da yawa suna ta’addanci ne kawai domin su samu abinda za su ci, saboda wallahi wasunsu ko bacci basu iya yi saboda rashin kwanciyar hankali. In dai ka samu ka ci abinci to shikenan, saboda ko za a iya yin haƙuri da komai to shi fa abinci dole sai an ci shi.

Ya kamata gwamnati ta taimaka ta tsaya ta duba lamarin nan. Ba wai yaƙi da kashe-kashe kawai ake buƙata ba, ace yau ankashe yan ta’adda gobe a ce an kashe sojoji, tsayawa ya kamata a yi a gano matsalar, a gano me yake kawo wannan ta’addancin sai a yi maganinsa.

Amma idan yau ka kashe ɗan ta’adda, za ka same shi yana da ‘ya’ya biyar ko fiye da haka, to suma fa daga wannan lokacin ko basu wannan aikin dole za su ɗauki makami saboda idan aka gane mahaifinsu da aka kashe ɗan ta’adda ne, to al’umma za su guje su, su kuma basu da zaɓi wanda ya wuce su koma cikin ‘yanuwan mahaifinsu ‘yan ta’adda su cigaba sa ta’addanci, haka abun zai ta tafiya.

Mu tsaya mu yi gyara, mu yafe wa junanmu, mu koma tsarin da muka baro a baya shekara da shekaru, mu kyautata wa junanmu, mu zauna lafiya, mu nemi arziki cikin tsanaki, mu bauta wa ubangijinmu cikin natsuwa da farin ciki, a wannan lokacin duk abunda muka roka zai bamu nan take. Ya Allah ka dawo muna da dauwamammen zaman lafiya da kwanciyar hankali mai ɗorewa a yankin Arewacin Nijeriya dam a Duniya bakiɗaya.

Kwamared Yusuf Muhammad Dosara, jami’in hulda da jama’a na Ɗaliban jami’ar jihar Zamfara (NUZAMSS). Ya rubuto daga jihar Zamfara.
08146672630
Imel: [email protected]

By Editor