Waiwaye: Allah Ya kama ni idan na koma APC, cewar Matawalle a 2019

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau

A ranar Talata, 29 ga Yunin da ya gabata gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Gwamnan ya ba da sanarwar komawsrsa APC ne
yayin wani ƙasaitaccen gangami da aka shirya don karɓar sa a APC ƙarƙashin jagorancin shugan jam’iyyar na ƙasa, Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe.

Matawalle, ya zama gwamnan Zamfara ne a 2019 biyo bayan wani hukunci da Kotun Ƙoli ta yanke kan rikicin cikin gidan da APC ta yi fama da shi a lokacin zaɓen fidda gwani a 2019.

Yayin gangamin an ji Matawalle na cewa, “Daga yau, ni Bello Matawalle Maradun, Gwamnan Zamfara, na farin cikin bayyana cewa na sauya sheƙa daga PDP zuwa APC. Daga yau na zama cikakken ɗan APC kuma shugabanta a Zamfara.

“Ina kira ga dukkan masu ruwa da tsaki na APC a jihar da su haɗa hannu da ni wajen gina jam’iyyar da kuma cigaban jihar.”

Sai dai kuma, idan za a iya tunawa a 2019, an ji inda gwamnan ya sha rantsuwar ba zai taɓa barin PDP ba, har da cewa Allah Ya kama shi idan ya yi yunƙurin yin hakan.

A cikin wani hoton bidiyo da jaridar SaharaReporters ta mallaka, an ji inda Matawallen ke cewa, “Na rantse da Allah, idan na munafunci PDP, kada in kwana lafiya a sauran lokutan rayuwata.

“Allah Ya kama ni idan na yi yunƙurin barin PDP ko munafuntar mambobinta.”

Lamarin da da daman ‘yan ƙasa musamman ‘yan jihar Zamfara ke kallo da gwamnan ya yi amansa ya koma ya lashe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *