Xi Jinping da shugaban AU sun taya juna murna

Daga CMG HAUSA

Yau Jumma’a ne, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, da shugaban karɓa-karɓa na ƙungiyar tarayyar Afirka AU, kana shugaban ƙasar Senegal Macky Sall, suka aika wa juna sakon murnar cika shekaru 20 da kafa AU da ƙulla alaƙar diflomasiyya tsakanin ƙasar Sin da AU.

Shugaba Xi ya ce, alaƙar Sin da AU na dada haɓaka, wadda ta taka muhimmiyar rawa wajen zurfafa dankon zumunta tsakanin Sin da Afirka, da ƙara faɗaɗa haɗin-gwiwarsu a sabon zamanin da muke ciki.

Ya ce yana fatan haɗa kai tare da Macky Sall da sauran shugabannin ƙasashe membobin AU, don tabbatar da aiwatar da nasarorin da aka cimma a wajen taron ministoci karo na 8 na dandalin tattaunawar haɗin gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC, da ci gaba da marawa juna baya a wasu muhimman batutuwa, da ƙara wakilcin ƙasashe masu tasowa a harkokin ƙasa da ƙasa, a kokarin bayar da gudummawa ga raya al’ummomin Sin da Afirka masu kyakkyawar makoma ta bai daya a sabon zamanin da muke ciki.

A nasa ɓangaren, Macky Sall ya ce, a daidai lokacin da ake cika shekaru 20 da kafa ƙungiyar AU, shugaba Xi Jinping ya aiko da sakon murna, al’amarin da ya shaida irin dadadden zumuncin dake tsakanin al’ummomin Afirka da Sin.

Ya sake jaddada cewa, Afirka na tsayawa haiƙan kan manufar kasancewar ƙasar Sin ɗaya tilo a duniya, da nuna cikakken goyon-baya wajen raya al’ummomin Sin da Afirka masu kyakkyawar makoma ta bai ɗaya.

Mai fassara: Murtala Zhang

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *