2023: Atiku ne zai ci Kano ba Kwankwaso da Tinubu ba — Shekarau

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Sanatan Kano ta Tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau ya sha alwashin cewa shi zai kawo wa ɗan takarar shugabancin qasa a Jam’iyar PDP, Atiku Abubakar ƙuri’u mafi rinjaye a Jihar Kano sama da na Rabi’u Kwankwaso na NNPP da Bola Tinubu na APC a zaven 2023.

Shekarau ya bayyana hakan ne a wata hira da a ka yi da shi a gidan talabijin na AIT a ranar Talata.

Tsohon gwamnan Kano ɗin ya ce yana da ɗumbin masoya ‘yan dangwale, waɗanda su ne su ka zaɓe shi a zaɓen 2003, lokacin da ya kayar da Kwankwaso, da kuma 2007.

Hakan ne Shekarau ya bayyana yaƙinin cewa masoyan na sa suna nan kuma su za su zaɓi Atiku Abubakar a 2023.

”A shekarar 2003 na kayar da Kwankwaso da Ganduje a takarar kujerar gwamna a Kano lokacin a Jam’iyyar ANPP, na basu ratar sama da ƙuri’a dubu ɗari shida.

“Sannan a zaɓen 2007 sun sake tsayawa takarar gwamna na kayar da su, don haka a zaɓen 2023 zan kawo wa Atiku quri’ar jihar Kano Insha Allah,” inji Shekarau.

Shekarau wanda kwanan nan ya sauya sheƙa daga Jam’iyyar NNPP zuwa PDP, ya kuma ƙara da cewa zai haɗo kan mutanensa na jihohi daban-daban da ke ƙasar nan, waɗanda su ka zave shi lokacin da ya yi takarar shugaban ƙasa domin su zavi Atiku Abubakar ko a wacce jam’iyya suke a zaɓe mai zuwa.